NNPP na Neman Jika Wa Kwankwaso Aiki, Ta Rubuta Wasika ga Hukumar INEC
- Bangaren NNPP da ke adawa da Rabiu Kwankwaso ya rubuta wasika zuwa ga hukumar zabe mai zamanta kanta (INEC)
- A wasikar, tsagin NNPP ya bukaci INEC da ta yi watsi da shirin 'yan Kwankwasiyya na gudanar da babban taro na kasa
- Hakan dai na zuwa ne bayan bangaren da ke goyon bayan jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ya fara shirin zaben shugabanni
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar NNPP ta bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ‘yan Najeriya su yi watsi da zaben shugabanni da tsagin Kwankwasiyya ke shirin yi.
Bangaren NNPP ya roki INEC da kar ta amince da shirin 'yan Kwankwasiyya karkashin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tana mai bayanin cewa hakan ya karya doka.

Source: Facebook
Punch ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Bangaren Jam’iyyar NNPP, Mista Ogini Olaposi, ya fitar yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsagin Kwankwaso na shirin babban taro
Ogini Olaposi ya ce NNPP ta riga da ta kammala zaben shugabanni kamar yadda kotu ta umurta a gudanar.
Hukumar Labarai ta Najeriya (NAN) ta tattaro cewa bangaren Kwankwaso ke jagoranta ta rubuta wa INEC takarda son sanar da ita shirinta na gudanar da zaben shugabanni da taro na kasa daga 25 ga Nuwamba zuwa Janairu 2026.
Sai dai Ogini Olaposi ya ce tsagin 'yan Kwankwasiyya ba shi da hurumin gudanar da zaben shugabanni a madadin NNPP domin yarjejeniyar da aka kulla tsakaninsu tun kafin zaben 2023 ta riga ta kare.
Tsagin NNPP ya sake taso Kwankwaso a gaba
Ya kuma jaddada korar da NNPP ta yi wa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a 2023, da wasu daga cikin yan Kwankwasiyya saboda aikata ayyukan da suka saba wa jam’iyya.
“Har yanzu muna mamakin yadda mutum irin Kwankwaso zai nace sai ya kwace jam’iyyar da ta ba shi dama kyauta ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.”
Bangaren NNPP ya yi kira ga INEC da ta cika aikinta na bin dokokin kotu da kuma sabunta sahihin jagorancin jam’iyyar a shafinta.
Ana zargin Kwankwaso da raina kotu
“Babbar Kotun Abia da Babbar Kotun Abuja sun tabbatar da korar Kwankwaso da magoya bayansa daga dukkan harkokin cikin gida na NNPP.
“Abin bakin ciki ne yadda Kwankwaso ya ki mutunta hukuncin kotu tare da yin watsi da shi," in ji Olaposi.
Jam’iyyar ta zargi tsohon shugabancin INEC da gazawa, tana mai bayyana fatan cewa sabon shugabanci zai nisanta kansa daga saba dokokin kasa, cewar rahoton Gazettengr.

Source: Facebook
NNPP ta cika baki kan karfin Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya cika baki kan tasirin da Rabi'u Musa Kwankwaso ke da shi a siyasa.
Hashimu Dungurawa ya ce APC ba ta da karfi a fagen siyasa da za ta samu damar cin zaben shekarar 2027 ba tare da taimakon Kwankwaso ba.
Ya bayyana cewa tattaunawar da ake cewa APC na yi da Kwankwaso ba gaskiya ba ce, kuma haduwa da wasu ’yan siyasa kawai suka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

