APC Ta Kammala Taron Kwanaki 4, an Tsara Yadda za a Samu Nasara a Zaɓen 2027

APC Ta Kammala Taron Kwanaki 4, an Tsara Yadda za a Samu Nasara a Zaɓen 2027

  • Shugabannin APC na Kano sun kammala zaman tattaunawar kwanaki hudu domin tsara dabarun zaben 2027
  • Tsohon shugaban jam'iyya, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun fara shirin mara wa Shugaba Bola Tinubu baya
  • An umarci hukumomin jam’iyya a kananan hukumomi da gundumomi su buɗe ofisoshin APC domin ƙarfafa siyasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugabannin jam’iyyar APC na Kano sun kammala taron kwanaki hudu da aka shirya domin haɗa kan jiga-jigai daga dukkannin kananan hukumomin jihar kafin zaben 2027.

Taron wanda tsohon gwamna kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranta, ya gudana ne a gidansa da ke Kano.

APC ta yi babban taro a Kano
Shugabannin APC yayin taro a Jihar Kano Hoto: Sani Gilashi Haruna
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa wakilai daga APC na Kano ta wasu jihohin Arewa domin karfafa tafiyar siyasa kafin babban zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje, 'yan APC sun fitar da 'dan takarar shugaban kasa da suke so a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta yi taro a Kano

Jaridar Vanguard ta ruwaito Ganduje ya bayyana cewa wannan taron ya kasance na musamman domin dawo da haɗin kai da kuma daidaita tsakanin ƴan jam'iyya.

Gwamnan ya ƙara da cewa haka kuma taron zai tabbatar da biyayya ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin da siyasar 2027 ke ƙara kwararowa.

Ganduje ya ce:

“A cikin kwanaki ukun nan, burinmu shi ne mu tabbatar da cikakkiyar ɗa’a da haɗin kan jam’iyya daga sama har ƙasa, kuma mu tabbatar da goyon bayanmu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu."

Ya ce wakilan jam’iyya sun nuna ƙwazo wajen daidaita tafiyar APC domin ta ci gaba da zama jam’iyya mai rinjaye a Kano da Najeriya baki ɗaya.

Kiran Abdullahi Ganduje da ƴan APC

Ganduje ya ce shugabannin APC daga kananan hukumomi 44 sun nemi izini domin fara mara wa Tinubu baya a matsayin ɗan takarar APC guda ɗaya a 2027.

Kara karanta wannan

Sanata kalu: "Mun gano dalilan da suka sa aka dawo da satar dalibai"

Ya ce:

"Mun yanke shawarar cewa kowace Karamar Hukuma za ta tara shugabannin jam’iyya da magoya baya domin bayyana goyon baya ga Shugaba Tinubu a fili.
Ganduje ya ce an yi shirin samun nasara a zaben 2027
Tsohon Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Facebook

A wani bangare na farfado da jam’iyyar, Ganduje ya umurci a buɗe dukkanin ofisoshin APC a kananan hukumomi 44 da gundumomi 484 domin su zama wuraren ƙarfafa alaka da jama'a.

Ya ce jam’iyyar za ta ɗauki ƙwararrun masu aikin fasaha domin shirin rajistar ‘yan jam’iyya ta hanyar zamani, la’akari da cewa Kano ce ta fi kowace jiha yawan masu rajista a baya.

Ya ce:

"Kowace Karamar Hukuma za ta samar da kwararru guda uku, za mu horas da su a hedikwatar jiha domin yi wa ƴan jam'iyya rajista."

APC ta gargadi karamin Ministan gidaje

A baya, mun wallafa cewa reshen jam’iyyar APC na jihar Kano ya gargadi karamin ministan gidaje, Yusuf Ata, kan kalaman da ake zargin na iya haifar da baraka a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Daruruwan 'yan NNPP sun watsewa Kwankwaso a Kano, sun koma APC

Gargadin da shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya fitar ta ce ya yi takaicin Yusuf Abdullahi Ata dangane da goyon bayan takarar Sanata Barau Jibrin a zaben 2027 mai zuwa.

Ministan ya bayyana goyon bayansa ga Sanata Barau, tare da kira ga sauran ‘yan jam’iyya — ciki har da tsohon dan takarar gwamna na 2023, Nasiru Yusuf Gawuna — su mara masa baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng