Minista Ya Yi Zazzafan Martani ga APC a Kano, Ya Koya Mata yadda Ake Siyasa

Minista Ya Yi Zazzafan Martani ga APC a Kano, Ya Koya Mata yadda Ake Siyasa

  • Karamin ministan harkokin gidaje a Najeriya ya yi martani mai zafi game gargadin da jam'iyyar APC ta yi masa
  • Abdullahi Ata ya mayar da martanin ga APC a Kano, yana cewa maganganunsa na baya ba su saba ka'ida ba
  • Rt. Hon. Ata ya ce rubuta wasiƙa zuwa shugaban ƙasa a lokacin matsanancin tsaro ba daidai ba ne kwata-kwata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Karamin Ministan Harkokin Gidaje, Abdullahi Ata ya mayar da martani kan gargadin APC a jihar Kano.

Rt. Hon. Abdullahi Ata ya yi martanin yana jaddada cewa maganganunsa ba su keta wata doka ta jam’iyya ba.

Minista ya yi martani ga APC a Kano
Karamin ministan gidaje, Abdullahi Yusuf Ata. Hoto: Abdullahi Ata.
Source: Facebook

Ata ya ce ya yi magana ne cikin haƙƙinsa na faɗar ra’ayi, ba domin haifar da rikici ba, inda ya ce an fahimce su ba daidai ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: APC ta gargadi minista, Ata kan tallata takarar Barau a 2027

Martanin Ata ga APC a jihar Kano

Wasiƙar da APC ta aika, wadda Abdullahi Abbas ya sanya wa hannu, ta zarge shi da magana kamar kakakin jam’iyya da haddasa rashin jituwa tsakanin mambobi.

Sai dai Atah ya bayyana cewa ya rubuta martani domin wayar da kan jama’a, tare da nanata gaskiyar biyayyarsa ga jam’iyya da shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Ya ce fitar da irin wannan wasiƙa, musamman a lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsaro, na iya karkatar da hankali daga abubuwan gaggawa na ƙasa.

Atah ya tuna cewa shugaban ƙasa ya dakatar da tafiye-tafiyen kasashen waje domin kula da tsaro, kuma ya kamata shugabanni su mayar da hankali kan haɗin kai da zaman lafiya.

Ya ce kasancewarsa Minista kuma ɗan jam’iyya ba ya hana shi haƙƙin faɗar ra’ayinsa na dimokuraɗiyya game da makomar jam’iyya ko batutuwan siyasa.

Minista ya yi martani bayan gargadin APC a Kano
Shugaban APC, Abdullahi Abbas da ministan gidaje, Abdullahi Yusuf Ata. Hoto: Yusuf Ata|Salihu Tanko Yakasai.
Source: Facebook

Dalilin biyayya ga Tinubu da Ata ke yi

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Atiku da Kwankwaso sun fadawa Tinubu matakan da ya kamata ya dauka

Atah ya kara da cewa biyayyarsa ga Shugaba Tinubu da APC tabbatacciya ce, sannan duk wani zargi na neman tayar da husuma ba shi da tushe.

Ya ce idan fadar gaskiya game da dabarar jam’iyya a 2027 na nufin kuskure a idon wasu, to yana yi ne saboda kishin jam’iyya, cewar rahoton The Guardian.

Dangane da goyon bayan sa ga Barau Jibrin, ya ce wannan ra’ayi ne nasa na kansa, ba sanarwar jam’iyya ba, kuma domin amfaninta ne.

Ya bayyana Barau a matsayin ɗan takara mafi ƙarfi da zai iya maida APC kan mulkin Kano a 2027, bisa gogewa da kwarewar siyasar ƙasa.

Ya ce irin wannan tunani mai zurfi ya dace jam’iyya ta karɓa domin tsara dabarun nasara kafin fara tsaida ‘yan takara a hukumance a matakin jam’iyya.

Atah ya jaddada cewa ba ya neman karɓe ikon jam’iyya, kuma maganganunsa nazari ne na siyasa da kowa zai iya yarda ko jin haka cikin dimokuraɗiyya.

Kano: Daruruwan 'yan NNPP sun koma APC

Kun ji cewa majiyoyi sun ce mambobin jam’iyyar NNPP da dama sun koma APC a gundumar Rimin Gado a Kano.

Kara karanta wannan

Kungiyar CAN ta yi magana bayan sace dalibai a Niger, ta ba Kiristoci shawara

Rabiu Sulaiman Bichi da ya karbe su ya bayyana cewa matakin ya nuna sun dauki muhimmiyar shawara ta siyasa.

Shugaban wadanda suka sauya sheka, Mohammad Karofin-Yashi, ya bayyana dalilin da ya sa suka dauki matakin shiga APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.