Siyasar Kano: APC Ta Gargadi Minista, Ata kan Tallata Takarar Barau a 2027
- Ana zargin jam’iyyar APC a Kano ta gargadi karamin ministan gidaje, Yusuf Ata, kan tallata burin takarar Sanata Barau Jibrin
- A cikin wata sanarwa da ta fitar, jam’iyyar ta ce furucinsa na iya haifar da rikici da rashin jituwa a tsakanin mambobi
- APC ta yi barazanar daukar matakin ladabtarwa idan ministan bai daina irin wannan maganganu na siyasa ba a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Reshen APC na jihar Kano ya gargadi karamin ministan gidaje, Yusuf Ata, ana zargin hakan bai rasa nasaba da tallata burin zama gwamna na Sanata Barau Jibrin.
Wannan gargadi ya biyo bayan wata hira da ministan ya yi, inda ya bayyana goyon bayansa ga takarar Barau.

Source: Facebook
Rahoton Daily Nigerian ya nuna cewa Ata ya kira sauran ’yan jam’iyya, ciki har da tsohon dan takarar gwamna a 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, su mara wa Sanata Barau baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan bayyana wannan matsaya, jam’iyyar APC a jihar Kano ta fito da wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na jihar, Abdullahi Abbas, ya sanya wa hannu.
Jam'iyyar APC ta gargadi ministan gidaje
Jam’iyyar ta ce irin kalaman ministan suna cikin abubuwan da za su iya raba kan ’yan jam’iyyar da tada rikici a cikinsu.
A cikin sanarwar da jam’iyyar ta fitar, ta ce:
“Shugabancin jam’iyyar APC ya lura da wasu kalaman da ka yi a kafofin yada labarai game da harkokin cikin jam’iyya da kuma masu neman mukami a cikinta.
"Wadannan kalamai suna da alamar kawo rashin fahimta da sabani a tsakanin mambobi.”
Jam’iyyar ta kara da cewa duk wata magana da ta shafi harkokin cikin gida na jam’iyya tana karkashin shugabancin jam’iyyar da kuma kakakinta.
Ta kara da cewa irin wannan magana ba ta cikin hurumin wasu da ba su da wannan iko ko matsayi na doka a tsarin jam’iyya.
Premium Times ta ce APC ta jaddada cewa ministan bai da damar magana ta yada matsayar jam’iyya a bainar jama’a kamar yadda ya yi.
Abin da ya kamata Yusuf Ata ya yi
Sanarwar ta bayyana cewa ministan gidajen yana da damar goyon bayan duk wanda yake so a siyasance.
Sai dai ta ce matsayin da yake rike da shi na zama mamba a majalisar zartarwa ta tarayya yana bukatar kiyaye kalamai masu kawo rarrabuwar kai.

Source: Facebook
Jam’iyyar ta ce ya kamata ministan ya rika mayar da hankali kan al’amuran da za su karfafa hadin kai a cikin jam’iyya.
APC ta yi barazanar daukar mataki kan Ata
APC ta kammala da cewa idan ministan ya ci gaba da irin wannan furuci, jam’iyyar za ta dauki matakin da ya dace da tanadin dokokinta.
Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa za su dauki matakin ne domin kare hadin kai da mutuncin APC a Kano da kasa baki daya.
Sai dai a takardar, jam'iyyar ba ta fito baro-baro ta ambaci laifin da tsohon shugaban majalisar dokokin na jihar Kano ya aikata ba.
'Yan NNPP sun koma APC a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa mutane sama da 700 ne suka sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa NNPP a Kano.
Shugaban masu sauya shekar ya bayyana cewa sun dauki matakin ne bayan dogon nazari kuma za su jawo wasu 'yan NNPP zuwa APC a gaba.
Dr. Rabiu Bichi da ya karbe su ya bayyana cewa za a cigaba da ba su dama a cikin jam'iyyar ba tare da wariya ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


