PDP Ta Fara Adawa Mai Zafi, Ta Ragargaji Tinubu kan Sace Dalibai a Kebbi

PDP Ta Fara Adawa Mai Zafi, Ta Ragargaji Tinubu kan Sace Dalibai a Kebbi

  • PDP ta yi kira ga shugaba Bola Tinubu ya je jihar Kebbi da sauran wuraren rikice-rikice domin ƙarfafa rundunonin tsaro
  • Ta ce soke ziyararsa zuwa Afirka ta Kudu da Angola ba zai magance matsalar tsaro da ke ƙara ƙamari a kasar ba
  • Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnatin APC da yin jawabai kawai ba tare da daukar mataki mai ma’ana ba bayan kai hari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta caccaki shugaba Bola Ahmed Tinubu kan fasa tafiya kasashen waje bayan hare-hare a jihohi.

Jam'iyyar PDP ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara jihohin da rikice-rikicen tsaro suka addaba, musamman Kebbi.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugaban PDP
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Tanimu Turaki na PDP. Hoto: Bayo Onanuga|Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Source: Facebook

Sakataren yada labaran PDP na kasa, Ini Ememobong ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin jam'iyyar na Facebook.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Tinubu ya umarci Matawalle ya tattara kayansa ya koma Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta nemi Tinubu ya tare a Kebbi

Ini Ememobong ya bayyana cewa matsalar sace dalibai 25 na makarantar Maga da kuma ƙaruwar tashin hankalin Arewa ya nuna cewa Bola Tinubu ba ya magance matsalolin tsaro.

Ya ce bai kamata Tinubu ya ci gaba da zaman jin daɗi a cikin fadar shugaban kasa ba a irin wannan lokaci mai matuƙar muhimmanci.

A lokacin da ta ke bukata Tinubu ta koma Kebbi, PDP ta ce:

“Koma wa jihohin da ake rikici zai sanya jami’an tsaro su ɗauki matakan gaggawa wajen kawo karshen ta’asar da ake yi.”

PDP ta ce hakan zai ƙara kuzari a bangaren dakarun da ke yaki da ’yan ta’adda, musamman a yankunan da ake fama da hare-hare a kwanakin nan.

Sanarwar ta ci gaba da cewa shugabanci a irin wannan hali ba ya bukatar jawaban tausayi ko soke tafiye-tafiye kawai, ta ce ana son matakin da zai dawo da kwarin guiwa ga ’yan ƙasa.

Kara karanta wannan

Kiraye kiraye sun yawaita, ana son Tinubu ya yi murabus daga shugabancin Najeriya

PDP ta ce rashin tsaro ya yi kamari

Jam’iyyar PDP ta ce hare-haren kwanan nan a jihar Kwara ya sake tabbatar da cewa rashin tsaro ya zama jiki ga ’yan Najeriya.

Ta zargi gwamnatin APC da fitowa da bayanan da ba su kawo karshen matsalar ba bayan kai harin, tare da yin alkawura marasa amfani.

Business Day ta rahoto cewa PDP ta ce soke tafiyar shugaban kasa zuwa ƙasashen ketare ba ya nufin cewa gwamnati ta fara aiki gadan-gadan.

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa
Sabon shugaban PDP, Tanimu Turaki. Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Source: Facebook

Jam'iyyar ta ce idan da rikicin siyasa ne, kamar batun jihar Rivers, da Tinubu ya yi duk mai yiwuwa wajen magance shi, amma ya matsalar tsaro na ƙara girma.

Kokarin Tinubu kan masalar tsaro

A wani rahoton, mun kawo muku cewa gwamnatin Najeriya ta ce shugaban kasa Bola Tinubu ya dukufa wajen magance matsalar tsaro a fadin kasar.

Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

Ran maza ya baci: Tinubu ya umarci sojoji su ruguza 'yan ta'adda a Najeriya

Mohammed Idris ya bayyana cewa shugaban kasar ya ba dakarun soji umarni su gaggauta ceto daliban da aka sace a jihar Kebbi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng