'Abin da Ya Sa APC Ke Neman Taimakon Kwankwaso': NNNP Ta Tona Asiri
- Shugaban NNPP na reshen jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya cika baki game da karfin siyasar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Ya zargi APC da rikicewa tare da neman tallafin Kwankwaso, yana mai cewa NNPP yanzu ta shahara, kuma zabukan 2027 za su zama daban
- Dungurawa ya kare jam’iyyarsa, ya yaba wa gwamna Abba Kabir kan kasafin 2026, kuma ya ce NNPP na shirin tunkarar 2027 da karfi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Shugaban NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya yi magana kan tasirin da Rabi'u Musa Kwankwaso ke da shi.
Dr. Hashimu Dungurawa ya ce APC ba ta da karfi a fagen siyasa da za ta samu damar cin zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Source: Twitter
Dungurawa ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a hedikwatar NNPP wanda Daily Trust ta bibiya.
Dungurawa ya bayyana tasirin Kwankwaso a siyasa
Shugaban jam'iyyar ya zargi APC na Kano da tarayya da rasa shugabanci, abin da ya sa suke neman taimakon Kwankwaso.
Ya ce wadannan ’yan jam'iyyar APC sun rikice kuma sun san ba tare da Kwankwaso ba, ba za su yi nasara a zaben 2027.
Dungurawa ya bayyana cewa tattaunawar da ake cewa APC na yi da Kwankwaso ba gaskiya ba ce, kuma haduwa da wasu ’yan siyasa kawai suka yi.
Da yake mayar da martani kan kuri’un NNPP a Kano a 2023, ya ce jam’iyyar sabuwa ce sosai, kuma wayar da kai ci gaba da gudana.
Ya ce tambarin jam’iyyar ba ta fito fili a takardar zabe ba, amma duk da haka NNPP ta samu kujeru a Kano, Jigawa, Taraba da Bauchi.

Source: Twitter
NNPP ta magantu kan zaben cike gurbi
Dungurawa ya ce sabon tambarin NNPP da karuwar shahararta a yanzu za su sa zaben 2027 ya banbanta, tare da karfafa tushen jam’iyyar.
Ya kara da cewa yawancin shugabannin jam’iyyar za su ci gaba da rike mukamansu bisa kundin tsarin NNPP, muddin ba su bar jam’iyya ba, cewar Punch.
Ya bayyana cewa zaben cike gurbi zai gudana don maye gurbin kansiloli uku da suka rasu a Garin, Dala da Doguwa cikin watan mai zuwa.
Yabon da NNPP ta yi wa Abba Kabir
Shugaban NNPP ya yabawa Gwamna Abba Kabir kan kasafin 2026, yana cewa ya mayar da hankali kan ilimi da noma tare da manyan ayyukan gine-gine a Kano.
Ya caccaki gwamnatin Abdullahi Ganduje, yana zargin ta da sakaci kan batun ilimi, tallafin karatu da kuma bashin fansho da ’yan jihar ke fuskanta.
Dangane da canjin jam’iyya, ya ce dan majalisa daya ne kacal ya fice da kansa, sauran tuni an dakatar da su kafin su bar jam’iyyar.
Kwankwaso ya magantu kan sace daliban Kebbi
Kun ki cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa don magance karuwar rashin tsaro.
Sanata Kwankwaso ya nuna damuwa kan sace dalibai 25 a Kebbi, kisan Janar M. Uba a Borno da kuma yin garkuwa da mutane da yawa a Zamfara.
Ya kuma koka a kan yadda aka samu 'yan ta'adda suna kutsa wa wasu kananan hukumomi da ke gefe da garuruwan da ke fama da rashin tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


