El Rufai Ya Hango Makomar Gwamnonin da Ke Komawa APC a Zaben 2027
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi tsokaci kan babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Nasir El-Rufai ya bayyana cewa sauya shekar da wasu gwamnoni ke yi APC, ba za ta hana 'yan Najeriya zaben shugabannin da suke so ba
- Tsohon gwamnan ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su shiga jam'iyyar ADC domin ceto kasar nan daga halin da ta tsinci kanta a ciki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi magana kan yawan sauya shekar da wasu gwamnoni ke yi zuwa jam'iyyar APC.
Malam Nasir El-Rufai ya ce yawan sauya shekar da gwamnonin ke yi, ba zai hana ’yan Najeriya zabar shugabannin da suke so a zaben 2027 ba.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa jigon na jam’iyyar ADC ya bayyana hakan a yayin bude ofishin tuntuɓa da wayar da kai na ADC na kasa da aka yi a Jos, ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me El-Rufai ya ce kan masu sauya sheka?
Ya ce yayin da gwamnonin jam’iyyar PDP ke komawa APC, ’yan Najeriya kuwa suna komawa ADC.
El-Rufa’i ya bayyana cewa ADC na da cikakkiyar damar hada kan al’ummar Plateau idan ta karɓi jagorancin jihar da ma Najeriya baki daya a 2027.
Tsohon gwamnan ya ce komai bai tafiya daidai a halin yanzu, amma har yanzu akwai fata.
Ya yi kira ga mazauna jihar su mara wa ADC baya domin ta samu damar karɓar mulki a jihar da kuma kasa baki ɗaya.
“Shekaru 40 da suka gabata ina zuwa Plateau kusan kowane mako saboda wacce zan aura a lokacin tana yin NYSC a Jos. Har bayan aure muna ziyartar Jos a karshen mako. Amma daga lokacin abubuwa sun lalace a Jos, Plateau.”
“Ina fatan idan aka samu kyakkyawan shugabanci a jiha da kasa, za mu iya hada kan al’ummar Plateau daga kowace kabila da addini, domin jihar ta koma wurin zaman lafiya da yawon bude ido kamar yadda muka sani. Muna rokon Allah Ya ba mu ikon hada kan ku.”
- Nasir El-Rufai
'Yan Najeriya za su kada gwamnoni
Ya ce ’yan Najeriya ba sa jin daɗin jagorancin PDP da APC, don haka suna neman sabon shugabanci, yana mai cewa da goyon bayan jama’a ADC za ta kayar da APC mai mulki a babban zabe na gaba.
“Na san kowa ya gaji da gwamnatin APC da PDP a fadin kasa. Kowa ya jingina da ADC domin ta ceci Najeriya. Gwamnonin PDP na komawa APC amma ’yan Najeriya na komawa ADC. Da ikon Allah, ’yan Najeriya miliyan 230 za su kayar da gwamnoni 25.”
“’Yan Najeriya sun yanke shawarar cewa a 2027 za su zabi ADC. Abin da ya rage shi ne mu hada kai mu tara ’yan jam’iyya gaba daya, mu fito da kyawawan ’yan takara da manufofi masu amfani ga ’yan kasa.”
- Nasir El-Rufai

Source: Twitter
El-Rufai ya ja hankalin matasa
El-Rufa’i ya kara jan hankalin matasa da mata, inda ya bayyana cewa:
“Kowane mutum a nan na da rawar da zai taka. ADC ita ce jam’iyyar kadai da ta ware kashi 40 na mukaman jagoranci ga matasa, da kashi 35 ga mata masu neman mukami. Jam’iyya ce ta matasa da mata.”
Tsohon shugaban PDP ya koma ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban PDP a jihar Kwara, ya yi murabus daga ci gaba da zama mamba a jam'iyyar.
Hon. Babatunde Mohammed ya raba gari da jam'iyyar PDP mai adawa ne bayan kwashe fiye da shekara 20 a cikinta.
Hakazalika, tsohon shugaban na PDP wanda ya kuma taba zama shugaban majalisar dokokin jihar, ya sanar da komawarsa zuwa jam'iyyar ADC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


