‘Ban Aikin Albashi Na’: Hadimin Shugaban Majalisa Ya Ajiye Aikinsa Wata 9 da Nadinsa
- Wani mai taimakawa Kakakin Majalisa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ajiye aikinsa bayan dogon tunani kan matsaloli da suka shafi siyasa
- 'Dan siyasar ya ce rashin samun damar aiwatar da al’amura da ake bukata a matsayin SLA ya tilasta shi ajiye mukamin
- Abbas ya godewa Hon. Usman Bello Kumo bisa damar da ya ba shi, yana mai cewa zai sanar da matakin siyasarsa nan gaba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Daya daga cikin masu taimakawa kakakin majalisar dokokin Najeriya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ajiye aikinsa.
Hon. Muhammad Abubakar Auwal Akko ya yi murabus ne bayan dogon nazari wanda ya zama dole duba da wasu matsaloli da suka dabaibaye mukamin.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa ta musamman da Hon. Auwal Akko ya turawa wakilin Legit Hausa a yau Laraba 19 ga watan Nuwambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin shugaban majalisa ya fadi dalilin murabus
Hon. Akko ya yi godiya bisa samun damar da ya yi domin kasancewa daya daga cikin masu taimakawa kakakin majalisar (SLA).
A cikin sanarwar, Akko ya ce:
"Na ajiye aikina a matsayin mai taimakawa a ofishin kakakin majalisa, mukamin da na samu ta hanyar Hon. Usman Bello Kumo.
"Tun daga lokacin da aka nada ni, babu wani aiki, nauyi ko jadawalin da aka taba damka min a hukumance, wannan ya jefa ni cikin damuwa, musamman wajen karɓar albashi ba tare da aiki ba, abin da ya saba da tarbiyya ta ta aiki, gaskiya da rikon amana.
"Wannan mataki ya biyo bayan tunani mai zurfi da kuma neman hanyar inganta aikina, siyasa da kuma wasu bukatu na karan kaina, akwai wasu abubuwa game da mukamin musamman rashin ba ni dama kan wasu lamura da ci gaban siyasa ta, rayuwa, matsin lamba da nake samu daga masu ruwa da tsaki a mazaba ta, sun sanya dole na ajiye wannan aiki."

Source: Facebook
Godiyar da Akko ya yi ga Hon. Kumo
Jiogn APC ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa matakin ya zama dole duba da batutuwan da ya jero wadanda ke dakile siyasarsa.
Har ila yau, ya mika godiya ta musamman ga dan majalisar tarayya a mazabar Akko a jihar Gombe, Hon. Usman Bello Kumo wanda ya yi masa sanadin samun mukamin.
"Ganin haka, ya zaman dole na ja baya domin kare martaba ta, siyasa da kuma aikin da nafi kwarewa kansa.
"Ina godiya ga Hon. Usman Bello Kuma game da wannan dama da ya ba ni, kuma ina neman afuwa ga duk wanda wannan mataki zai batawa rai, zan sanar da matakin da ya dace game da siyasa ta bayan tattaunawa."
- Muhammad Auwal Akko
Legit Hausa ta tattauna da yaron hadimin
Shamsudden Sani ya yi maraba da murabus da Hon. Akko ya yi inda ya tabbatar da cewa hakan zai ba shi dama domin ba da gudunmawa ga al'umma fiye da a yanzu.

Kara karanta wannan
Bayan kashe kashen mutane, Tinubu ya tura jakadiyar wanzar da zaman lafiya Filato
Ya ce:
"Duk abin da za ka yi, za ka yi domin ci gaba, musamman a siyasa ana koko don riba ne, murabus na Architect abu ne da aka zauna aka yi dogon lissafi.
"Muna ganin shi Akko matashi ne kuma akwai rawar da zai taka sosai a siyasa, kasancewarsa a waccar inuwar gaskiya an tauye bai samun damarmaki har a gane baiwar da Allah ya ba shi a siyasa."
Shamsudden ya ce ko ba shi matsayin da aka yi wata manufa su ma suka duba ga maganr yan shan miya sun yi kane-kane.
Rigima na neman barkewa a majalisa
A baya, mun kawo muku rahoton cewa wasu 'yan Majalisar wakilai sun nuna bacin ransu kan ma'aikatan da aka dauka aiki kwanan nan da kuma ayyukan mazabu.
A cewarsu, shugabannin Majalisar na yin abubuwa da dama ba tare da tuntubarsu ba, sannan babu wasu ayyuka a mazabunsa.
Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a majalisar wanda wasu ke ganin zai iya kawo tarin matsaloli idan ba a dauki mataki ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

