Tirkashi: Shugaban Jam'iyyar PDP, Ƴan Majalisa 16, Kwamishinoni 22 Sun Koma APC
- An samu guguwar sauya sheka mai karfi a Taraba yayin da gaba daya shugabannin PDP, suka koma APC a rana guda
- Zaɓaɓɓun ‘yan majalisa 16, shugabannin kananan hukumomi 16, kwamishinoni da jami’an gwamnati duk sun bar PDP
- Masana sun ce wannan hijira ta siyasa ta zama mafi girma tun kafuwar jihar, yayin da ake jiran matakin Gwamna Kefas Agbu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Alhaji Abubakar Bawa, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Taraba, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a kasa.
Wannan na zuwa ne yayin da ake jiran Gwamna Agbu Kefas ma ya koma APC, duk da cewa ya dage bikin sauya shekar sakamakon sace ɗalibai mata a jihar Kebbi.

Source: Twitter
Taraba: PDP ta rasa shugabanci a rana 1
Kazalika, dukkan kwamishinoni da mambobin majalisar zartarwa ta jihar Taraba sun bi sahu wajen barin PDP, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihar Taraba ta shiga yanayi na rikicin siyasa mafi girma tun bayan kafuwar ta, bayan da wasu manyan ‘yan siyasa suka fara fita daga PDP cikin zuga.
Tun daga safiyar Talata takardun murabus suka fara taruwa a hedikwatar jam’iyyar, ofisoshinta na kananan hukumomi da gundumomi.
Lokacin da rana ta take, sai ya bayyana a fili cewa PDP ta rasa kusan dukkan manyan jagororinta a fadin jihar Taraba.
Sauya shekar 'yan majalisa da ciyamomin Taraba
Hankalin PDP ya fara girgiza ne lokacin da dukkan 'yan majalisar dokoki 16 na jam'iyyar suka yi murabus ba tare da bata lokaci ba.
Bayan wannan, shugabannin kananan hukumomi 16 karkashin shugabancin ALGON, Dr. Aminu Jauro Hassan, suka sanar da ficewarsu daga PDP.
Sun ce wannan mataki ne don su daidaita da tafiyar siyasar Gwamna Kefas da kuma goyon bayan “Shirin samar da ci gaba” na gwamnatinsa.

Source: Twitter
Shugabannin jam’iyya da wasu kusoshi sun bar PDP
Shugaban PDP na jihar, Alhaji Bawa Abubakar, da dukkan shugabannin jam’iyyar a matakin jiha suma sun yi murabus, abin da masana suka ce cikakkiyar rugujewar PDP ce a Taraba.
Daga baya kuma kwamishinoni, mashawarta, da manyan jami’an gwamnati da dama suka sanar da komawarsu APC, in ji rahoton Daily Post.
Kwamishinar yada labarai, Barr. Zainabu Usman Jalingo, ta tabbatar da cewa dukkannin mambobin majalisar zartarwa sun koma APC.
Wasu daga cikin kwamishinonin sun ce barin PDP ne zai ceci makomarsu, saboda matsalolin cikin gida da rikicin shugabanci a jam’iyyar ta kasa.
Yanzu dai ana jiran Gwamna Kefas Agbu ya sanya ranar da za a yi gangamin shigarsa jam'iyyar APC, lamarin da zai kawo karshen mulkin PDP a Taraba.
Gwamna Kefas ya dage komawa APC
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamna Agbu Kefas ya dakatar da sauya shekarsa zuwa APC saboda sace ‘yan matan makaranta a Kebbi.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da Shugaba Bola Tinubu da su dauki matakan gaggawa domin ceto yaran da aka sace cikin koshin lafiya.
A makon da ya gabata ne gwamna jihar na Taraba ya sanar da shirinsa na barin PDP zuwa APC a ranar Laraba, 19 ga Nuwamba, 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

