Gwamna Kefas Ya Dakatar da Shirin Shiga Jam'iyyar APC, Ya Fadi Dalili

Gwamna Kefas Ya Dakatar da Shirin Shiga Jam'iyyar APC, Ya Fadi Dalili

  • Gwamna Agbu Kefas na Taraba ya dakatar da sauya shekarsa zuwa APC saboda sace ‘yan matan makaranta a Kebbi
  • Ya yi kira ga jami’an tsaro da Shugaba Tinubu da su dauki matakan gaggawa domin ceto yaran da aka sace cikin koshin lafiya
  • A makon da ya gabata ne Gwamna Kefas ya sanar da shirinsa na barin PDP zuwa APC a ranar Laraba, 19 ga Nuwamba, 2025

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya shelanta cewa ya dakatar da shirinsa na shiga jam’iyyar APC mai mulki a ranar Laraba mai zuwa.

Ya bayyana cewa bai dace a gudanar da babban bikin siyasa irin wannan a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar mummunan lamari na sace ɗalibai mata a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Ran APC ya baci, ta dura kan PDP bayan saboda taimakon Trump a Najeriya

Gwamna Agbu Kefas ya dakatar da shirin sauya shekarsa zuwa APC.
Gwamnan Tabara, Agbu Kefas a wurin taron majalisar zatarwar jiharsa a Jalingo. Hoto: @GovAgbuKefas
Source: Twitter

Gwamnan Taraba ya damu da sace daliban Kebbi

Gwamna Kefa Agbu ya ce mafi muhimmanci a yanzu shi ne tausayawa iyalan yaran da aka sace, da kuma karfafa masu gwiwa, in ji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kefas ya ce wannan lokaci ne da ya kamata zumunci, haɗin kai da tausayawa juna su tsaya a gaba fiye da harkokin siyasa.

Ya lura cewa matsalolin tsaro sun sake tasowa a sassa daban-daban na ƙasar, kuma ya zama dole shugabanni su nuna halin in-kula ga jin daɗin jama’a sama da komai.

Gwamnan ya ce, tun farko gwamnatinsa ta sanya tsaro, ilimi da kare marasa galihu a matsayin tubalan mulkinsa, saboda haka ya ga ya dace ya janye duk wani babban taron siyasa har sai an warware lamarin daliban da aka sace.

Kiran gwamna ga Tinubu da jami'an tsaro

A jawabin nasa, Gwamna Kefas ya yi addu’a tare da mika sakon jaje ga iyalan yaran da aka yi garkuwa da su a makarantar Kebbi.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun fitar da matsaya kan daliban Kebbi da aka sace

Ya kuma mika sakon goyon baya ga gwamnatin Kebbi da al’ummar jihar baki ɗaya, yayin da ya ce nauyin ceto yaran ya rataya har a wuyan Shugaba Bola Tinubu.

Yayin da ya jinjinawa kwarewar jami'an tsaron Najeriya, ya ce yana da yakinin jami'an za su yi duk mai yiwuwa don ganin sun ceto 'yan makarantar Kebbi da aka sace.

Gwamnan ya kuma roki ‘yan Najeriya da su kasance masu natsuwa da fahimta, musamman a irin waɗannan lokutan da ƙasa ke fuskantar kalubale.

Gwamna Agbu Kefas ya ce zai sanar da sabuwar ranar shiga APC bayan lamura sun daidaita.
Hoton Gwamna Kefas Agbu na Taraba zaune a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Jalingo. Hoto: @GovAgbuKefas
Source: Twitter

Gwamna ya fasa taron shiga jam'iyyar APC

Gwamnan Taraba ya bayyana cewa, a yanzu ya fasa shirya taron koma wa jam'iyyar APC, har zuwa lokacin da al'amura za su daidaita.

Sanarwar ta ce gwamnan zai sanya sabuwar ranar shirya taron shigarsa APC bayan ya yi shawarwari tare da ganin an samu daidaito.

Kefas ya kara da cewa wanda ke rike da mukamin gwamnati dole ne ya fifita jin kai da tausayi fiye da bukatun siyasa a cewar Punch.

Wannan dakatarwar na zuwa ne bayan Kefas ya bayyana aniyarsa ta barin jam’iyyar PDP zuwa APC makon jiya, inda aka shirya taron karɓar sa a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya daukarwa iyayen yaran da aka sace alkawari

'Ba ruwan 'yan bindiga' - Gwamna Kefas

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Agbu Kefas ya bayyana gaskiya kan yadda aka kashe ƴar uwarsa, Atsi Kefas a hanyar zuwa Abuja a 2024.

Kefas ya ce wani ɗan sanda da ke gadin ayarin mahaifiyarsa ne ya ɗana bindiga, ya harbi ƴar uwarsa daga kusa-kusa, amma ba ƴan bindiga ba ne.

Galibin mazauna jihar Taraba sun ɗauka ƴan bindiga ne suka faramaki mahaifiyar gwamnan da yar uwarsa da nufin yin garkuwa da su, har sai da aka ji bayanin Kefas.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com