Mulki da Mulki: Gwamna Bala, Makinde da Wike Sun Yi Cirko Cirko a Hedkwatar PDP
- Ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Bala Mohammed, Seyi Makinde da Tanimu Turaki sun ki barin hedkwatar PDP
- Rahoto ya nuna cewa jiga-jigan sun zauna cikin motocinsu, kowane bangare na jiran sai daya ya bar harabar ofishin kafin ya tafi
- Hakan dai ya biyo bayan rigimar da aka yi tsakanin tsagin Wike da na Turaki, lamarin da ya kai ga jibge jami'an tsaro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigera - Rahotanni sun nuna cewa manyan kusoshin bangarori PDP sun ki fi fita daga hedkwatar jam'iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja duk da umarnin kami'an tsaro.
Jami'an tsaro da aka tura wurin sun yi kokarin shawo kan rikicin da ya barke tsakanin tsagin Wike da Turaki, tare da umartar duka shugabannin PDP sun tattara su bar harabar Wadata Plaza.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Bala Mohammed, Gwamna Seyi Makinde da shugaban PDP na kasa, Tanimu Turaki SAN sun ki barin hedkwatar jam'iyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike da gwamnonin PDP su ja daga a Abuja
Duka su uku suna zaune a cikin motar Gwamna Bala na jihar Bauchi yayin da a gefe guda, Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ki tafiya, ya zauna a cikin motarsa.
An ruwaito cewa yanzu haka wadannan jiga-jigai sun kekashe kasa sun ki barin harabar hedkwatar PDP duk da umarnin jami'an tsaro, kowane bangare na jiran sai dayan ya tafi.
Tun da farko, Sanata Samuel Anyanwu, wanda ke jagorantar bangaren Wike, ya isa Wadata Plaza tare da magoya baya.
Yayin da tsagin Wike ke shirin fara taro, sai su Gwamna Bala Mohammed, Makinde da mambobin NWC karkashin shugaban PDP, Tanimu Turaki suka dura wurin.
Da zuwansu suka kutsa kai cikin dakin taron NEC suka kuma sanar da cewa duba da rikicin da ke gudana, an dage zaman majalisar amintattu (BoT) da kwamitin zaratrwa (NEC) zuwa gobe.

Kara karanta wannan
"Ba kisan kiristoci kadai ake ba," Turaki ya bukaci Amurka ta kawo dauki Najeriya
Zuwan Wike ya kara lalata lamarin
Yayin da su Gwamna Bala, Makinde da Turaki za su tashi, sai ga Wike ya iso cikin izza da nuna isa, ya kutsa kai cikin harabar dakin taron da jami’an tsaro suka mamaye.
Ganinsa ya sa gwamnonin biyu da Turaki suka ƙi barin hedikwatar, duk da umarnin jami’an tsaro na cewa kowa ya bar wurin.

Source: Twitter
Gwamnonin sun bayyana cewa ba za su tafi ba muddin Wike yana nan, inda suka ce dole shi ma ya kama gabansa.
A halin yanzu, jami’an tsaro sun rufe hanyoyi, yayin da bangarorin jam’iyyar biyu na ci gaba da takaddama kan ikon mallakar hedikwatar PDP, cewar rahoton Punch.
Turaki ya tura sako ga Shugaba Trump
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki ya yi gargadin cewa abin da ministan Abuja, Nyesom Wike ke yi barazana ce ga dimokuradiyya.
Turaki ya tura sako ga Shugaban Amurka, Donald Trump, da wasu manyan ƙasashen duniya kan rikicin siyasar Najeriya.
Tsohon ministan ayyuka na musamman, Turaki ya yi gargadin cewa matukar ba a dauki mataki cikin gaggawa ba “dimokuraɗiyyar ƙasar nan na fuskantar barazana.”
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

