"Ba Kisan Kiristoci Kadai Ake ba," Turaki Ya Bukaci Amurka Ta Kawo Dauki Najeriya
- Sabon shugaban PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki ya yi gargadin cewa abin da ministan Abuja, Nyesom Wike ke yi barazana ce ga dimokuradiyya
- Kabiru Turaki ya bukaci shugaban Amurka, Donald Trump da sauran kasashen duniya su shiga tsakani domin ceto Najeriya
- Wannan kalamai na Turaki na zuwa ne bayan an ba hammata iska tsakanin magoya bayan tsagin Wike da na shi a Abuja yau Talata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya tura sako ga Shugaban Amurka, Donald Trump, da sauran ƙasashen duniya kan rikicin siyasar Najeriya.
Kabiru Turaki ya dauki wannan matakin ne bayan fadan da ya kaure tsakanin bangarensa da na ministan Abuja, Nyesom Wike a hedkwatar jam'iyyar PDP da ke Wadata Plaza a Abuja.

Source: Twitter
Vanguard ta ruwaito cewa sabon shugaban PDP ya yi kira ga Shugaba Trump na Amurka da sauran kasashen duniya su kawo dauki kan rigimar siyasar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Turaki ya zargi Wike da turo yan ta'adda
Tsohon ministan ayyuka na musamman, Turaki ya yi gargadin cewa matukar ba a dauki mataki cikin gaggawa ba “dimokuraɗiyyar ƙasar nan na fuskantar barazana.”
Turaki yi wannan furuci ne a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai kafin bangaren da yake jagoranta ya yi yunkurin gudanar da zaman NWC a Wadata Plaza.
Tanimu Turaki ya zargi Minista Wike, da kawo “yan ta’adda dauke da makamai” tare da wasu jami’an ‘yan sanda da nufin hana jam’iyyar PDP gudanar da harkokinta.
Sakon da shugaban PDP ya tura Amurka
Ya ce lamarin ya kai wani mataki da dole duniya ta tsoma baki domin shawo kan komai tun kafin abin ya wuce haka tabarbarewa ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Shugaban jam'iyyar PDP ya ce:
“Ina kira ga Shugaba Donald Trump, abin da ke faruwa ba kawai maganar kisan Kiristoci ba ce. Ya zo ya ceci dimokuraɗiyya a Najeriya. Ina kira ga dukkan ƙasashen da suka ci gaba, ku zo ku ceci Najeriya.”

Source: Getty Images
Rikicin cikin PDP ya kara ta'azzara
Turaki ya kara da cewa shugabannin jam’iyyar APC sun shirya tsaf kuma za su iya “su sadaukar da rayukansu” domin kare dimokuraɗiyya da amanar da aka ba su.
Rikicin cikin gida na PDP na kara ta'azzara yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da ikirarin mallakar ikon jam’iyyar, lamarin da ke barazana ga makomar adawa da tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Zanga-zanga ta barke a hedkwatar PDP
A wani rahoton, kun ji cewa magoya bayan tsagin ministan Abuja a rigimar PDP sun fantsama zanga-zangar adawa da sabon shugaban jam'iyyar na kasa, Tanimu Turaki.
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun daga kwalayen da nuna adawa da shugabancin Turaki, masu dauke da sakonni kala daban-daban da ke nuna ba sa goyon bayansa.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Irabor ya tsoma baki kan rigimar Wike da matashin soja a Abuja
Tuni dai jami'an rundunar 'yan sanda suka mamaye wurin domin dakile duk wata barazana da iya tasowa a hedkwatar jam'iyyar hamayyar da ke birnin tarayya Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

