Abu Ya Kacame, Sabon Shugaban PDP da Tsagin Wike na Iya Arangama a Taro
- Sabon shugabancin PDP ƙarƙashin Kabiru Tanimu Turaki zai gudanar da taron farko na kwamitin gudanarwa a ranar Talata a sakatariyar jam’iyya
- A lokaci guda kuma, tsagin Muhammad Abdulrahman da ke samun goyon bayan Nyesom Wike ya kira zaman gaggawa na kwamitin zartarwa
- Sai dai Turaki ya ce waɗanda suka kira taron - bangaren Wike ba ‘ya’yan jam’iyyar ba ne, yana mai cewa PDP za ta kare kanta daga masu kutse
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kabiru Tanimu Turaki, sabon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, ya bayyana cewa shugabancinsa zai gudanar da taron farko na kwamitin gudanarwa na kasa (NWC).
Za a gudanar da taron a ranar Talata a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja yayin da ake takaddama da tsagin Nyesom Wike da aka kora.

Source: Twitter
Premium Times ta bayyana cewa Turaki ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da manema labarai a Abuja bayan ganawar da ya yi da Kwamishinan ‘yan Sanda, Dantawaye Miller.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta kacame gabanin taron jam'iyya
Daily Post ta wallafa cewa Turaki, wanda ya taɓa rike kujerar Ministan Ayyuka na Musamman, ya ce an gayyaci gwamnoni na jam’iyyar, sanatoci da ‘yan majalisar wakilai.
Haka kuma ya gayyaci shugabannin kwamitin amintattu, shugabannin jihohi da sauran jiga-jigai domin halartar taron.
Ya ce sun sanar da ‘yan sanda batun taron ne a matsayin jam’iyya mai bin doka tare da tabbatar da cewa hukuma ta san da batun.

Source: Twitter
Sai dai hedikwatar PDP da aka tsara gudanar da taron, nan ne wurin da bangaren Muhammed Abdulrahman, wanda ke da goyon bayan Ministan Abuja Nyesom Wike zai yi nasa taron.
Tuni tsagin, ta bakin Sakataren Jam’iyya Samuel Anyanwu, ya kira zaman gaggawa na kwamitin zartarwa da kwamitin amintattu da BoT a rana guda.
Duk da korar su da aka yi a babban taron jam’iyyar da ya gudana a Ibadan, Anyanwu ya ci gaba da ikirarin cewa shi ne Sakataren jam'iyya, inda ya ce umarnin kotu da ke dakatar da korarsu.
Turaki ya soki bangaren Wike
Shugaban PDP, Turaki ya bayyana cewa mutanen da ke kiraye-kirayen zaman NEC da BoT ba su da hurumin yin hakan domin ba 'ya'yan jam'iyya ba ne musamman bayan an kore su.
Ya ce shugabancin jam’iyyar ba zai rufe ofis da jami’an tsaro ba, domin su ne za su shiga su ci gaba da gudanar da ayyukan jam’iyyar.
Turaki ya kara jan hankali cewa su a shirye suke su kare jam’iyyar da rayukansu idan har aka nemi hana su shiga sakatariyar.
Ya tabbatar da cewa taron zai fara da karfe 10 na safe, kuma an riga an aika da takardun gayyata. Ya kuma ce kwamishinan ‘yan sanda ya ba su tabbacin tsaro da kariya a ranar taron.
Turaki ya mika batun PDP ga 'yan sanda
A baya, mun wallafa cewa sabon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Kabiru Tanimu Turaki SAN, ya kai ziyara hedikwatar rundunar ’yan sandan Najeriya da ke Abuja gabanin taronsu.
Turaki da tawagarsa sun kai korafi kan tsohon sakataren jam’iyyar da aka kora, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu mutane da jam’iyyar ta zargi da kokarin tayar da rigimar cikin gida.
Idan ba a manta ba, PDP ta kori Anyanwu da wasu manyan jiga-jigai 10, daga ciki har da Ministan Abuja, Nyesom Wike, da tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


