'Dan Ganduje Ya Yi Ruwan Kayan Arziki a Kano, 'Yan Kwankwasiyya 500 Sun Koma APC

'Dan Ganduje Ya Yi Ruwan Kayan Arziki a Kano, 'Yan Kwankwasiyya 500 Sun Koma APC

  • Sama da mutane 3,000 ne suka ci gajiyar shirin tallafin da Umar Abdullahi Ganduje, dan tsohon shugaban APC ya kirkiro a Kano
  • Umar ya raba kayayyaki da suka hada da Keke Napep da kayan noma na zamani domin taimaka wa mutane su dogara da kansu
  • Bayan haka, tsohon 'dan takarar majalisar wakilan tarayyar ya kuma karbi mambobin NNPP 500 da suka sauya sheka zuwa APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Ɗan tsohon shugaban APC, kuma Babban Daraktan Sashen Fasaha na Hukumar Bunkasa Wutar Lantarki a Karkara ta Kasa (REA), Umar Abdullahi Ganduje, ya tallafawa magoya baya sama da 3,000 a jihar Kano.

Umar, ɗan tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da mataki na farko na shirin tallafin ne a wurin taron da aka gudanar a Armani, Kano, a daren Lahadi.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na kasa, Turaki ya kai korafin wasu jiga jigai wurin yan sanda

Dan tsohon gwamnan Kano, Umar Ganduje
Hoton dan tsohon shugaban APC na kasa, Umar Abdullahi Ganduje a wurin raba kayan tallafi a Kano Hoto: Umar Abdullahi Ganduje
Source: Facebook

The Nation ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Kakakin Tsohon Shugaban APC, Edwin Olofu, ya fitar a Abuja ranar Litinin.

Umar Ganduje ya tallafawa 'yan Kano

Kayan tallafin da aka raba wa matasa daga duka kananan hukumomi 44 sun haɗa da kayan noma da sauran kayan bunƙasa aikin gona domin taimaka wa mutane su dogara da kai.

Umar ya ce wannan tallafi “kadan ne daga abin da ya shirya” domin akwai manyan shirye-shiryen tallafi da ya tanada musamman ga matasa da mata a fadin jihar Kano.

Umar da aka fi sani da Abba Ganduje ya bayyana cewa burinsa na taimakon jama’a ne ya sa ya kirkiro shirin, ba wai ga mutanen mazabarsa ta Tofa/Dawakin-Tofa/Rimingado kaɗai ba, har ma ga al'ummar Kano baki daya.

Kayan da Abba Ganduje ya raba a Kano

'Dan siyasar ya kuma bayyana cewa za a ƙaddamar da zagaye na biyu na shirin nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Naira tiriliyan 1.4 sun yi ƙafa a CBN, an taso gwamnan babban banki ya yi bayani

A sanarwar da ya wallafa a Facebook, Umar ya ce:

“Mun riga mun fara shirye-shiryen mataki na gaba na wannan tallafi, wannan ba shi ne na karshe ba, duk wani ɗan APC da bai samu a yau ba, kada ya damu, lokaci zai zo,” in ji shi.

Kayan da aka raba sun haɗa da, Keke Napep, kananan motocin dako, takin zamani, magungunan kashe ciyawa, ingantattu iri, na’urorin sola, injin ban ruwa da sauransu.

Dan Ganduje, Umar Abdullahi.
Hoton dan tsohon gwamnan Kano, Umar Abdullahi Ganduje da mambobin NNPP da suka rungumi APC Hoto: Umar Abdullahi Ganduje
Source: Facebook

'Yan NNPP 500 sun koma APC

Bayan rabon kayan, Umar Ganduje ya karɓi mutum 500 daga jam’iyyar NNPP da suka koma APC.

Ya tabbatar masu da cewa jam’iyyar APC za ta karɓe su hannu bibbiyu ba tare da nuna masu wariya ba.

“Mun yaba da jarumtarku ta gano gaskiya da shiga APC, jam’iyya mafi ƙarfi a Afrika,” in ji shi.

Shugaban APC ya nemi afuwa a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya nemi afuwar mazauna Fagge bayan kalamansa sun haifar da ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

PDP na dab da rasa Taraba, gwamna ya bayyana ranar da zai sauya sheka zuwa APC

Rahotanni sun ce kalaman Abdullahi Abbas sun harzuka wasu daga cikin shugabannin al'umma a Fagge, kuma har sun kai kara gaban kotu.

Sai dai duk da haka, Abbas ya jaddada cewa al'ummar karamar hukumar Fagge ba su fahimci abin yake nufi ba, amma ya na rokon gafararsu kan kalaman da ya fadi

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262