Rikicin PDP: Sanata Anyanwu Ya Dora Laifin Abubuwan da ke Faruwa kan Gwamnoni 7

Rikicin PDP: Sanata Anyanwu Ya Dora Laifin Abubuwan da ke Faruwa kan Gwamnoni 7

  • Jagoran tsagin PDP da ke goyon bayan ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya caccaki gwamnonin jam'iyyar
  • Sanata Samuel Anyanwu ya dora laifin duka rigingimun da suke faruwa a PDP kan kungiyar gwamnoni, yana mai cewa laifinsu ne
  • Ya kuma yi fatali da korarsa da aka yi daga PDP kuma ya tabbatar da cewa ba zai kai kara kotu ba saboda abin da ya kira karya doka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya - Jigon jam’iyyar PDP, Sanata Samuel Anyanwu, ya zargi kungiyar gwamnonin jam'iyyar da haifar da rikicin da ya dabaibaye ta a yau.

Sanata Anyanwu na daya daga cikin manyan jiga-jigan da jam'iyyar PDP ta kora a babban taronta na kasa da ya gudana a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Sanata Samuel Anyanwu.
Hoton tsohon sakataren PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu Hoto: @sensamanyanwu
Source: Twitter

Da yake magana a shirin siyasa na tashar Channels tv watau Politics Today, Anyanwu ya ce ba zai ɗauki alhakin rikicin da ke faruwa a jam’iyyar PDP ba.

Kara karanta wannan

PDP ta rikice: Gwamnoni 2 sun nesanta kansu daga korar Wike, Fayose daga jam'iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Anyanwu ya zargi gwamnonin PDP

Sanata Anyanwu, tsohon sakataren PDP na kasa ya yi ikirarin cewa gwamnoni bakwai da da suka rage a PDP ne suka janyo matsalolin da ake ciki a jam'iyya.

“Gaskiyar magana ita ce zan ɗora wa kungiyar gwamnoni alhakin duk abin da ke faruwa da jam’iyyarmu a yau,” in ji shi.

Lokacin da aka tambaye shi ko ya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a jam’iyyar, ya ce ya yi iya bakin kokarinsa.

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP sun tattara kayansu sun bar ta saboda yadda al’amura suka lalace.

Wane laifi gwamnoni suka yi a PDP?

Anyanwu ya yi ikirarin cewa a wani lokaci gwamnonin sun nemi a gyara kundin tsarin mulki domin a sanya su a matsayin wani muhimmin bangare na PDP.

A rahoton Vanguard, Anyanwu ya ci gaba da cewa:

“Gwamnoni sun so a gyara kundin tsarin mulkin jam’iyya a sanya kungiyarsu a matsayin wani bangare na jam’iyya. To, wa ke kokarin kashe PDP a haka?”

Kara karanta wannan

An samu rudani yayin da PDP ta zabi sabon shugaban jam'iyya na kasa a taron Ibadan

Anyanwu, wanda ya ayyana kansa a matsayin “mai ceton jam’iyya” ya yi zargin cewa yawancin gwamnonin suna harkar siyasa ta bayan gida.

“Zan gaya wa gwamnonin su bar jam’iyyar nan ta huta domin ko da kai ne kake samar da kuɗin tafiyar da PDP ba yana nufin ka lalata jam’iyyar ba.
"Ya kamata iyayen PDP da suka kafa ta, wadanda suka kai shekaru 80 a duniya su huta,” in ji Anyanwu.
Gwamnoni da shugabannin PDP.
Hoton wasu daga cikin gwamnonin PDP da jiga-jigai a wurin babban taron jam'iyyar a Ibadan Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Anyanwu ya yi fatali da korarsa daga PDP

Ya yi fatali da korarsa daga jam’iyyar PDP, yana mai cewa matakin bai da inganci kuma ba bisa ka’ida aka yi shi ba. A cewarsa, ba zai kai karar abin da ya kira “karya doka” kotu ba.

Anyanwu ya kuma zargi gwamnonin PDP da janyo rigima da kuma yin sulhu da APC.

Turaki ya kai korafin Anyanwu ga yan sanda

A wani labarin, kun ji cewa shugaban PDP na kasa, Tanimu Turaki ya ki korafi wurin rundunar yan sanda kan yunkurin Samuel Anyanwu da mutanensa da tada rikici a babban ofishin jam'iyya.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: PDP ta fatattaki Wike, tsohon gwamna da wasu da ke kawo mata cikas

Turaki, wanda ya zama shugaban PDP a taron Ibadan, ya ce ba za su bari wasu korarrun mambobin jam'iyya su karbe ragamar Wadata Plaza ba.

Ya ce PDP na so a samu kwanciyar hankali ne domin a gudanar da harkokin jam’iyya ba tare da rikici ko tada jijiyoyin wuya ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262