Shugaban PDP na Kasa, Turaki Ya Kai Korafin Wasu Jiga Jigai Wurin 'Yan Sanda

Shugaban PDP na Kasa, Turaki Ya Kai Korafin Wasu Jiga Jigai Wurin 'Yan Sanda

  • Jam'iyyar PDP ta shirin gudanar da taron kwamitin gudanarwa (NWC) na farko bayan zaben sababbin shugabanni a taron Ibadan
  • Shugaban PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki SAN da wasu manyan kusoshi sun kai ziyara hedkwatar 'yan sanda da ke birnin Abuja
  • A yayin wannan ziyara, Turaki ya ce sun shigar da korafi kan tsohon sakataren PDP da aka kora, Sanata Samuel Anyanwu da wasu jiga-jigai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sabon shugaban PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), tare da wasu manyan jagororin jam’iyyar, sun kai ziyara hedikwatar ƴan sandan Najeriya da ke Abuja a daren Litinin.

Wannan ziyara na zuwa ne awanni kadan bayan kammala babban taron PDP, wanda ya gudana a ranakun Asabar da Lahadi, 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025 a Ibadan.

Kara karanta wannan

Tanimu Turaki: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata a sani game da sabon shugaban PDP

Tanimu Turaki.
Hoton shugaban PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki yayin hira da yan jarida a hedkwatar yan sanda da ke Abuja Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Leadership ta rahoto cewa Turaki da tawagarsa sun shigar da korafi ga yan sanda kan tsohon sakataren jam’iyyar da aka kora, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba PDP ta kori Anyanwu tare da wasu kusoshinta ciki har da Ministan Abuja, Nyesom Wike; tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose da wasu mutum bakwai bisa zargin cin amanar jam’iyya.

PDP na shirin gudanar da taron NWC

Bayan ganawa da kwamishinan ƴan sandan Abuja, Turaki ya ce PDP ta sanar da ƴan sanda shirin gudanar da taron kwamitin gudanarwa (NWC) na farko a babban ofishinta da ke Wadata Plaza gobe Talata.

Ya ce wannan ziyarar wani bangare ne na shirin tunkarar taron kwamitin NWC na farko tun bayan kammala babban taron jam'iyyar a Ibadan.

Turaki ya ce:

"Za mu gudanar da taron farko na NWC gobe. Mun gayyaci dukkan manyan shugabanni da dattawan jam’iyya.”

Kara karanta wannan

Sule lamido ya fadi matsayarsa kan taron PDP da ya nemi kotu ta dakatar

Jam'iyyar PDP ta kai korafin wasu jiga-jigai

Shugaban PDP ya ce sun kai korafi ga ƴan sanda ne saboda wasu daga cikin wadanda aka kora suna yada cewa za su kira taron BOT da NEC, alhali ba su da hurumin yin hakan.

A rahoton Vanguard, Turaki ya ci gaba da cewa:

“Babban taron jam’iyya shi ne mafi girma wajen yanke hukunci, kuma ya yanke hukuncin korar wadannan mutane. Saboda haka ba su da wani matsayi ko iko a PDP.”
Sanata Samuel Anyanwu.
Hoton tsohon sakataren PDP da aka kora, Sanata Samuel Anyanwu Hoto: PDP Nigeria
Source: Facebook

Turaki ya ce PDP na so a samu kwanciyar hankali ne domin a gudanar da harkokin jam’iyya ba tare da rikici ko tada jijiyoyin wuya ba a hedkwatarta da ke Wadata Plaza.

Makarfi ya ajiye mukaminsa a BoT

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya yi murabus daga mukaminsa na sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BoT).

Sanata Makarfi ya bayyana cewa tsarin rabon mukamai da kuma kasancewar sabon shugaban jam’iyya na kasa ya fito daga yankinsa ne suka sa ya ajiye mukamin.

Kara karanta wannan

Saraki da wasu kusoshin PDP da suka ki halartar babban taron jam'iyyar a Ibadan

Makarfi ya tuna cewa tun watanni biyu da suka gabata ya yi kokarin yin murabus, amma shugabannin BoT suka roke shi da ya dakata har sai an kammala babban taron jam’iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262