Makarfi: Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Ajiye Mukaminsa a PDP, Ya Fadi Dalilin Murabus

Makarfi: Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Ajiye Mukaminsa a PDP, Ya Fadi Dalilin Murabus

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, ya yi murabus daga kan mukamin da yake da shi a jam'iyyar PDP
  • Ahmed Makarfi ya yi murabus ne daga kan mukamin sakataren kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar hamayyar
  • Tsohon Sanatan ya bayyana cewa tun a baya ya so daukar matakin amma aka tausasa zuciyarsa ya hakura

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya yi murabus daga mukaminsa na sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BoT).

Sanata Ahmed Makarfi ya bayyana cewa tsarin rabon mukamai da kuma samun sabon shugaban jam’iyya daga yankinsa ne suka sa ya yanke shawarar barin mukamin.

Ahmed Makarfi ya yi murabus daga mukaminsa a PDP
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi Hoto: Sen. Ahmed Makarfi
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa Ahmed Makarfi ya sanar da murabus dinsa ne cikin wata wasika da ya aikawa shugaban kwamitin amintattun PDP.

Kara karanta wannan

Tanimu Turaki: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata a sani game da sabon shugaban PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta samu sabon shugaban jam'iyya

A karshen mako, jam’iyyar ta PDP ta zabi Kabiru Tanimu Turaki, tsohon ministan harkoki na musamman, a matsayin sabon shugabanta na kasa.

An zabi Kabiru Tanimu Turaki ne yayin babban taron jam''iyyar na kasa da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Makarfi ya yi murabus a mukaminsa na PDP

Makarfi ya tuna cewa tun watanni biyu da suka gabata ya yi kokarin yin murabus, amma shugabannin BoT suka roke shi da ya dakata har sai an kammala babban taron jam’iyyar.

“Kusan watanni biyu da suka wuce na ajiye aiki a matsayin sakataren BoT, na kuma aike da sanarwa a dandalin WhatsApp na kwamitin."

- Sanata Ahmed Makarfi

Ya kara da cewa Wabara ya roke shi da ya ci gaba da zama har sai an zabi sabon shugaban jam’iyya, rahoton tashar Channels tv ya tabatar da labarin.

“Mai girma Shugaba kai ne ka roke ni da na tsaya har bayan kammala babban taron da zai samar da sabon shugaba.”

Kara karanta wannan

Sule lamido ya fadi matsayarsa kan taron PDP da ya nemi kotu ta dakatar

- Sanata Ahmed Makarfi

Meyasa Makarfi ya bar mukaminsa?

Ya bayyana cewa tun da dadewa yake da ra’ayin cewa ba daidai ba ne a samu shugaban jam’iyya da sakataren BoT daga yanki daya ba.

Yanzu da sabon shugaban jam’iyya ya fito daga Arewa maso Yamma, inda shi ma ya fito, Makarfi ya ce lokaci ya yi da zai matsa gefe.

Makarfi ya ajiye mukaminsa a jam'iyyar PDP
Ahmed Makarfi ya rike mukamin sakataren BoT na PDP Hoto: Abubakar Ibrahim Ango
Source: Facebook
“Babban dalilin da ya sa na yi murabus a wancan lokaci da yanzu shi ne cewa bai dace shugaban jam’iyya da sakataren BoT su fito daga yanki ɗaya ba."
“Yanzu da shugaban jam’iyya ya fito daga Arewa maso Yamma, wajibi ne na ba shi cikakkiyar damar gudanar da aikinsa."

- Sanata Ahmed Makarfi

Ya ce ya dauki wannan mataki ne don tabbatar da adalci da guje wa duk wani raishin daidaito cikin tsarin shugabancin PDP.

A karshe ya gode wa Wabara da sauran mambobin BoT bisa kyakkyawar alakar aiki da suka yi tare tsawon lokacin da ya jagoranci ofishin.

Kara karanta wannan

PDP ta rikice: Gwamnoni 2 sun nesanta kansu daga korar Wike, Fayose daga jam'iyya

Tsohon gwamna ya fice daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Idris Wada, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Idris Wada ya rike kujerar gwamnan Kogi daga Janairu 2012 zuwa Janairu 2016 a karkashin PDP, amma ya gaza lashe zaben tazarce.

Tsohon gwamna ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar APC ne a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2025 a gidansa da ke Odu, cikin karamar hukumar Dekina ta jihar Kogi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng