Sauya Sheka: Sanata Ndume Ya Hango Matsalar da Za Ta Samu Jam'iyyar APC

Sauya Sheka: Sanata Ndume Ya Hango Matsalar da Za Ta Samu Jam'iyyar APC

  • Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya yi tsokaci kan yawan sauya shekar da ake yi zuwa jam'iyyar APC
  • Ali Ndume ya nuna damuwa kan cewa masu sauya shekar ba su tabuka komai bayan sun samu kansu a cikin jam'iyyar
  • Hakazalika, sanatan ya bayyana matsalar da za ta iya faruwa da jam'iyyar APC saboda yawan sauka shekar da ake yi zuwa cikinta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa kuma sanatan Borno ta Kudu, Ali Muhammad Ndume, ya yi gargaɗi kan sauya shekar da ake yi zuwa jam'iyyar APC.

Sanata Ndume ya yi gargadin cewa jam’iyyar APC mai mulki na iya shiga mummunar matsala saboda yawan sauya shekar gwamnoni da ‘yan majalisa daga jam’iyyun adawa zuwa cikinta.

Sanata Ndume ya gargadi jam'iyyar APC
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume Hoto: Sen Mohammed Ali Ndume
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Ndume ya yi wannan jawabi ne a wajen taron lakcar shekara-shekara ta marigayi Dr. Nnamdi Azikiwe da aka gudanar a otal din NICON Luxury da ke Abuja, a daren ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Nentawe: Shugaban APC ya fadi jihar da jam'iyyar za ta kwace a zaben 2207

APC na samun masu sauya sheka

A kwanakin baya, gwamnonin Akwa Ibom (Umo Eno), Delta (Sheriff Oborevwori), Enugu (Peter Mbah), da Bayelsa (Douye Diri) duk sun fice daga PDP inda suka koma APC.

Haka kuma, APC ta samu fiye da kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar dattawa da wakilai saboda yawan masu sauya sheƙa.

Me Ndume ya ce kan sauya shekar?

Da yake karɓar lambar yabo a wajen taron, Ndume ya soki irin mutanen da ke shigowa jam’iyyar ba tare da kara mata komai ba.

“Na yi gargaɗin cewa APC tana cika ma kanta nauyi. Idan ka cika jirgin ruwa da kaya, musamman idan kayan ba su da amfani, jirgin zai iya kifewa. Idan ya kife, mamallakin jirgin shi ne zai shiga mawuyacin hali."

- Sanata Ali Ndume

Sanata Ndume ya ce yawancin masu sauya sheka ba sa bada wata gudunmawa bayan shigowa cikin jam’iyyar, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

Taron siyasa: Ƴan takarar gwamna, ƴan majalisun tarayya sun sauya sheka zuwa APC

“Wasu gwamnoni suna sauya sheka, nan take su zama shugabannin jam’iyya a jiharsu, amma sai su yi tsit ba sa tabuka komai."
"PDP na fama da rashin taka rawar da ta dace a fannin adawa, amma mu a APC ba mu lallashin kowa ya shigo. Su da kansu ne suke guduwa zuwa gare mu saboda inda suke ya kama da wuta."

- Sanata Ali Ndume

Sanata Ali Ndume ya ba 'yan Najeriya shawara
Sanata Ali Ndume a zauren majalisar dattawa Hoto: Sen Mohammed Ali Ndume
Source: Facebook

Ndume ya ba 'yan Najeriya shawara

Ndume ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su nuna goyon bayansu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Ndume ya bayyana cewa shugaban na da niyya mai kyau, sai dai ya nuna damuwar cewa wasu ministoci da manyan hadimai ba su da kwarewar da ake bukata wajen sauke nauyin da ke kansu.

A farkon taron, Mrs. Dame Azikiwe ta yi kira ga shugabannin siyasa na wannan zamani da su yi koyi da sadaukarwa da kishin kasa da shugabannin Jamhuriya ta farko suka nuna.

'Yan majalisar Taraba sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu karuwa a jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Da gaske Tinubu na ba 'yan adawa kudi su sauya sheka? Dan APC ya fito da bayanai

Shugaban majalisar dokokin jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Hakazalika, mambobi 15 na jam'iyyar PDP da ke a majalisar dokokin jihar Taraba sun sauya sheka zuwa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng