Ga Wata Sabuwa: Manyan 'Yan Siyasa 3 Sun Maka Shugaban Jam'iyyar APC a Kotu
- Wasu manyan shugabannin APC uku a Zamfara sun maka shugaban jam’iyyar na jihar, Tukur Danfulani, a kotu
- Babangida Shinkafi, Kabiru Ibrahim da Ibrahim Kurya sun shigar da karar ne bayan dakatar da su daga jam'iyyar
- Wadanda suka shigar da karar, sun bukaci babbar kotun jihar da ta dauki matakai hudu kan shugaban jam'iyyar APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Rikicin siyasa ya mamaye APC a Zamfara bayan an maka shugaban jam’iyya na jihar, Tukur Danfulani, a gaban babbar kotu da ke Gusau.
Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar guda uku ne suka yi karar Tukur Danfulani bayan sanarwar dakatar da su da aka yi daga APC.

Source: Twitter
Dalilin dakatar da wasu kusoshin jam'iyyar APC
A wata sanarwa da aka fitar a Abuja ranar Lahadi, wadanda abin ya shafa sun ce an dakatar da su ba bisa ka'ida ba, kuma hakan ya saba wa kundin tsarin jam'iyyar, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda aka dakatar su ne;
- Babangida Shinkafi, shugaban APC na gundumar Shinkafi ta Kudu
- Kabiru Ibrahim, sakataren kula da walwala na APC
- Ibrahim Kurya, wakilin masu nakasa a jam'iyyar APC
An ruwaito cewa, an dakatar da jagororin uku ne bayan halartar wani taron masu ruwa da tsaki da kungiyar Wamban Shinkafi ta shirya, watau tsagin siyasa da ke goyon bayan Dr. Sani Shinkafi.
Sai dai, an ce jam’iyyar APC ta jihar ta dauki halartar taron a matsayin wani yunkuri na yi wa jam'iyya zagon kasa, wanda ya kai ga dakatar da su.
“An dakatar da mu da baki ne kawai”
A cewar wadanda aka dakatar, an yi musu hukuncin ne ba tare da wata takarda ba, kuma shugaban karamar hukumar Shinkafi, Ibrahim Bama, ya yi hakan ba tare da ya fada musu laifin da suka aikata ba ko ya basu damar kare kansu ba.
Sun bayyana cewa:
“Ba daidai ba ne a hukunta ’yan jam’iyya saboda halartar taron masu ruwa da tsaki da aka shirya domin ci gaban jam’iyya.
"Wannan dakatarwar an fitar da ita ne daga ofishin shugaban APC na jihar Zamfara, Tukur Danfulani.”
Sun kara da cewa ba za su bari “makiyan jam’iyya” su karkatar da su daga manufarsu ba, kuma suna neman a dakatar da duk wani mataki har sai kotu ta yanke hukunci.

Source: Original
Abin da 'yan APC suke so kotu ta yi
A cikin karar da suka shigar ranar 14 ga Nuwamba, sun bukaci kotu ta, tabbatar da cewa su duka halastattun ’yan jam’iyyar APC ne.
Sun kuma nemi kotu ta rushe duk wani yunkuri na dakatarwa, korar su, tsoratarwa ko cin zarafinsu, kamar yadda rahootn Vanguard ya nuna.
Hakazalika, suna so kotu ta hana shugabannin jam'iyya daukar mataki na dindindin kan su, kuma a tilasta dukkan bangarori su ci gaba da tsayawa kan matsayin da ake kai yanzu har sai an kammala shari’ar.
Sun kuma jaddada cewa su zababbun shugabanni ne, da suka yi nasara a babban taron jam’iyyar na 2022, kuma har yanzu wa’adinsu bai kare ba.
An kori shugaban APC na Zamfara
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, an kori shugaban APC a jihar Zamfara, Tukur Danfulani daga muƙaminsa kan rashin iya shugabanci.
Shugaban jam'iyyar a gundumar Galadima, Garba Bello da wasu mutane 15 sun dauki matakin ne kan zarge-zarge da ake yi wa Danfulani.
Bello da mukarrabansa sun zargi Danfulani da rashin iya shugabanci, nuna wariya ga mambobi, da karkatar da ayyukan jam'iyyar ga wadanda ba 'yan APC ba ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


