Saraki da Wasu Kusoshin PDP da Suka Ki Halartar Babban Taron Jam'iyyar a Ibadan
- Yayin da PDP ke gudanar da babban taronta a Ibadan, wasu fitattun shugabanni da gwamnonin jam’iyyar ba su halarta ba
- Legit.ng ta tattaro jerin manyan shugabannin da suka taba rike muhimman mukamai da ba su bayyana a wurin taron ba
- Rashin halartar wadannan jiga-jigai ya haifar da muhawara kan ko PDP na fama da sabuwar rabuwar kai gabanin zaben 2027
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ibadan - Yayin da babban taron jam’iyyar PDP ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo, wasu fitattun shugabanni da ake sa ran ganinsu, ba su halarci taron ba.
Legit.ng ta duba jerin wadannan jiga-jigai da suka sha taka rawa sosai a siyasar jam’iyyar da kuma kasar baki daya.

Source: Twitter
Kusoshin PDP da ba su halarci taron Ibadan ba
1. Bukola Saraki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bukola Saraki ya taba rike mukamin Shugaban Majalisar Dattawa na 13 daga 2015 zuwa 2019. Ya zama Shugaban Majalisar dattawa ne a ranar 9 ga Yuni, 2015, a karkashin APC.
Kafin haka, ya yi gwamna a jihar Kwara daga 2003 zuwa 2011, sannan ya koma majalisar dattawa a 2011 a karkashin PDP, yana wakiltar Kwara ta Tsakiya. An sake zabensa a 2015 amma a APC.
A 2018, Saraki ya bar APC ya koma PDP, jam’iyyar da ya fara siyasa a cikinta. Sai dai duk da irin tasirinsa a PDP, ba a ganshi a taron jam'iyyar na kasa da ake gudanarwa ba.
2. Gwamna Siminalayi Fubara
Gwamna Siminalayi Fubara na Rivers ya fara mulki a 2023 a karkashin PDP. Amma a ranar 18 ga Maris, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi bayan ayyana dokar ta baci, inda ya sauya shi da Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas.
An dawo masa da mukaminsa ne a ranar 18 ga Satumba, 2025. Duk da kasancewarsa fitaccen jigo a PDP, shi ma bai halarci taron jam'iyyar na Ibadan ba, in ji rahoton Channels TV.
3. Gwamna Ademola Adeleke
Gwamna Adeleke na Osun ya ke mulki tun 2022 bayan lashe zaben da ya doke tsohon gwamna Isiaka Oyetola na APC.
Adeleke ya taba zama Sanata mai wakiltar Osun ta Yamma daga 2017 zuwa 2019. Duk da rikicin cikin gida da ke damun PDP, Adeleke ya ce zai samu tazarcensa a zaben Osun na 2026, yana mai cewa yana “ta tafiya cikin nasara.”
Sai dai har yanzu ba a gansa a taron kasa da jam’iyya ke gudanarwa ba, kuma bai fitar da wani jawabi game da rashin halartar ba.

Source: Facebook
4. Sule Lamido
Sule Lamido ya yi gwamna a jihar Jigawa daga 2007 zuwa 2015. Kafin haka ya rike mukamin Ministan Harkokin Waje daga 1999 zuwa 2003.
Lamido yana daga cikin jiga-jigan da suka yi suna a PDP tsawon shekaru, in ji wani rahoton jaridar Vanguard.
Duk da irin karramawa da girman sa a jam’iyya, shi ma bai samu hallara taron PDP a Ibadan ba, ko da yake, wasu na ganin saboda karar da ya shigar ne.
Gwamna Kefas zai bar PDP zuwa APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya kammala duk wasu shirye-shirya na sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Gwamna Kefas dai na daya daga cikin gwamnonin PDP da ba su halarci babban taron jam'iyyar na kasa da ke gudana a Ibadan, babban birnin jihar Oyo ba.
Yayin da ake maganar rashin halartarsa, gwamnan Taraba ya bayyana cewa zai fita daga PDP tare da shiga APC a hukumance ranar Laraba, 19 ga Nuwamba, 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


