‘Abin da Ya Sa Haduwar Siyasar Atiku da Kwankwaso ba Za Ta Taba Yiwuwa ba’

‘Abin da Ya Sa Haduwar Siyasar Atiku da Kwankwaso ba Za Ta Taba Yiwuwa ba’

  • Jigon jam'iyyar APC a Najeriya ya yi hasashe kan yiwuwar hadewar Rabiu Kwankwaso da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
  • Mataimakin shugaban APC a yankin Kudu ya ce duk da maganganun da suka taso hakan ba mai yiwuwa ba ne
  • Ya bayyana cewa Atiku “ya kai ƙarshen tafiyarsa ta siyasa”, yana mai cewa Kwankwaso ba zai yi haɗin gwiwa da shi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mataimakin Shugaban APC na Kudu maso Gabas, Ijeoma Arodiogbu, ya bayyana abin da yake ganin zai faru a siyasar Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar.

Arodiogbu ya karyata jita-jitar cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin yin kawance kafin 2027.

APC ta bayyana abin da zai faru a kawancen Atiku da Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Jigon APC ya magantu game da Kwankwaso, Atiku

Kara karanta wannan

'Ka da a ziyarci kabarina': Tsohon gwamna ya ba da wasiyyar yadda za a birne shi

A cikin hirarsa da Punch, Arodiogbu ya ce duk surutan da ake yi sun samo asali ne daga irin girmamawar da Atiku ya nuna wa Kwankwaso a lokacin bikin zagayen ranar haihuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arodiogbu ya ce babu wani lokaci da Kwankwaso zai bar jam’iyyarsa ya koma kowace hadaka tare da Atiku.

Ya ce Kwankwaso gogaggen ɗan siyasa ne wanda zai gane inda riba take amma zai yi wahala ya hada kai da Atiku.

An fadi inda Kwankwaso zai fi dacewa

Arodiogbu ya ce APC ta yi imani cewa Kwankwaso zai fi samun amfani idan ya koma jam’iyyar mai mulki.

Ya ce yiwuwar hakan na iya faruwa kafin karshen wannan shekarar, inda ya yi watsi da tunanin cewa zai yi kawance da Atiku.

Lokacin da aka tambaye shi ko Atiku zai iya ba wa Kwankwaso kariya ko dama mafi girma fiye da Tinubu, sai Arodiogbu ya yi martani mai zafi.

Ya ce babu abin da Atiku zai iya bayarwa, yana mai cewa kwazon siyasar Atiku ya riga ya kai ƙarshe.

Wasu na hasashen Atiku da Kwankwaso za su hade
Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Rade-radin da ake ta yadawa kan Kwankwaso

Maganganunsa sun zo ne a daidai lokacin da ake ta samun hasashen siyasa a Arewacin Najeriya, inda Atiku da Kwankwaso ke da ƙarfin tasiri.

Kara karanta wannan

Sowunmi ya hango wurin da gwamnatin Tinubu ta yi kuskure a rigimar Wike da matashin soja

Kwanan baya Atiku ya kira Kwankwaso “mai kishin kasa” a sakon taya shi murnar cika shekara 69, abin da ya ƙara hura wutar jita-jita.

Sai dai Kwankwaso ya fito fili ya musanta cewa ya rubuta takardar neman shiga APC, yana mai kiran duk waɗannan rahotanni “maganganun kan layi ne marasa tushe”.

Yayin da siyasa ta 2027 ke matsowa a hankali, masana sun ce dukkan bangarorin biyu na iya ci gaba da buɗe hanyoyin tattaunawa ba tare da bayyana hakan ba, musamman yadda APC ke ƙoƙarin ƙarfafa matsayin ta a Arewa.

NNPP ta soki Kwankwaso kan cin amana

Kun ji cewa tsagin NNPP ya ce Rabiu Kwankwaso ne ya jawo ficewar Abdulmumin Jibrin zuwa APC da Oluremi Oguntoyinbo zuwa PDP.

Sakataren tsagin NNPP, Ogini Olaposi, ya zargi Kwankwaso da aikata abin da ya kira “cin amanar jam’iyya” da kokarin karbe shugabanci.

Ya ce rikicin shugabanci da ke tsakanin Kwankwaso da wasu jiga-jigai na jam’iyyar ne ya janyo 'yan siyasa na sauya sheka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.