Turaki: PDP Ta Zabi Sabon Shugaban Jam’iyyar, Ya Fadi Yadda Zai Kawo Sauyi
- Tsohon ministan harkokin musamman ya lashe kujerar shugaban PDP na ƙasa bayan samun kuri’u 1,516 a taron Ibadan
- Sabon shugaban ya yi alƙawarin dawo da mulkin jama’a cikin jam’iyyar, yana mai cewa “ba za a sake zalunci ko raini ba”
- Sanatoci, gwamnoni da daruruwan jakadu daga jihohi 17 sun halarta, inda aka tabbatar da wasu sababbin shugabanni biyu a taron
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Tsohon Ministan Harkoki na Musamman da Hulɗa Tsakanin Gwamnati, Kabiru Turaki (SAN), ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa.
Turaki ya samu nasarar ne a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, inda ’yan takara daga jihohi 17 suka kada kuri’un su.

Source: Facebook
Yawan kuri'u da aka kada a zaben
Tsohon Sanatan Anambra ta Tsakiya, Ben Obi, ya bayyana cewa Turaki ya samu kuri’u 1,516 a yayin taron da aka yi a filin Lekan Salami, Ibadan, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: PDP ta fatattaki Wike, tsohon gwamna da wasu da ke kawo mata cikas
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Sanata Yakubu Danmarke ya samu kuri’u 275, yayin da kuri’u 43 suka lalace, a cewarsa, jimillar kuri’un da aka kada su 1,834 ne, amma Turaki ya yi nasara da tazara mai yawa.
Obi ya ƙara da cewa Solarin Adekunle ya yi nasara a matsayin Mataimakin Sakataren Shirye-shirye na ƙasa, inda aka fafata kan manyan kujeru guda biyu.
Ya bayyana cewa jimillar daliget 3,131 ne suka halarta, amma an tantance 2,745 daga cikinsu.

Source: Facebook
Alkawarin da Turaki ya daukawa PDP
A jawabin karɓar kujerarsa, Turaki ya ce ba zai yi sakaci da amincewar da aka yi masa ba inda ya tabbatar wa ’ya’yan jam’iyyar cewa zai gudanar da aikin da aka ɗora masa cikin gaskiya da rikon amana.
Yayin da yake duba tarihin PDP, ya ce jam’iyyar ita ce kaɗai babbar jam’iyyar da ta riƙe sunanta tun kafuwarta.
Ya jaddada cewa an kammala komawa ga jama’a, yana mai cewa:
“Ba za a ƙara zalunci ba a cikin PDP.”
Turaki ya ce jam’iyyar za ta fara sauraron ’yan Najeriya tare da mayar da martani kan abubuwan da suke buƙata, Ya yi alƙawarin ƙara haɗa kan jam’iyyar tare da jawo waɗanda suka bar PDP su dawo.
A cewarsa, PDP na da abubuwan da za ta fitar nan ba da jimawa ba, don farawa da gudanar da sababbin manufofinta.
PDP ta kori Wike, Fayose daga jam'iyyar
Mun ba ku labarin cewa jam'iyyar PDP mai adawa ta yi ta maza a taronta da aka gudanar a jihar Oyo inda ta sallami wasu daga cikin jiga-jiganta.
Daga cikin wadanda jam'iyyar ta tabbatar da korarsu akwai ministan Abuja, Nyesom Wike, Ayodele Fayose da ke kawo mata cikas.
Tsagin Wike ya yi ƙoƙarin dakatar da taron ta hanyar kotu, amma PDP ta samu hukuncin kotun Oyo da ya ba ta damar gudanar da taron.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
