PDP Ta Rikice: Gwamnoni 2 Sun Nesanta Kansu daga Korar Wike, Fayose daga Jam'iyya
- Gwamna Caleb Mutfwang da Gwama Ahmadu Fintiri sun nesanta kansu daga korar Nyesom Wike da Ayodele Fayose daga PDP
- Sun bayyana cewa matakin ya zo ne a lokacin da bai dace ba, kuma korar su Wike zai haifar da karin rabuwar kai a jam’iyyar PDP
- Gwamnonin sun jaddada cewa sulhu, shawarwari da haɗin kai su ne hanya mafi inganci wajen magance matsalolin PDP
Filato - Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya nesanta kansa daga korar ministan Abuja, Nyesom Wike daga jam'iyyar PDP.
Hakazalika, Muftanga ya ce babu hannunsa a korar tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose; tsohon sakataren jam’iyya na kasa, Samuel Anyanwu da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Source: Twitter
Gwamna ya magantu kan korar Wike daga PDP
Matsayar gwamnan na jihar Filato na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labara gidan gwamnatinsa, Gyang Bere, ya fitar a daren Asabar, in ji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, an rahoto gwamnan ya ce ba a tattauna batun korar Wike da manyan kusoshin jam'iyyar a taron kungiyar gwamnonin PDP ko a NEC kafin gabatar da shi ba.
Ya bayyana cewa wannan matakin bai dace ba, yana mai cewa korar manyan mambobi a wannan lokacin zai jefa jam’iyyar cikin karin rikici, ya kuma hana nasarar kokarin farfado da ita.
Gwamna Mutfwang ya ce wannan yunƙuri na iya zurfafa sabani a cikin gida, ya kuma hana kokarin da jam’iyyar ke yi na sake gina martabarta bayan jerin rikice-rikicen baya.
“Sulhu shi ne zai kawo ci gaban jam’iyya” — Mutfwang
Ya jaddada cewa sulhu, tattaunawa da dabarun baiwa juna dama su ne manyan hanyoyin warware rikici a jam’iyyar PDP.
Ya kuma yi nuni da cewa dole ne jam’iyyar ta mayar da hankali kan shirin daidaitawa da haɗa kan masu ruwa da tsaki, saboda duk wata sabani ana magance shi ne ta hanyar tattaunawa mai amfani, ba hargitsi ko tsaurin mataki ba.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: PDP ta fatattaki Wike, tsohon gwamna da wasu da ke kawo mata cikas
Gwamnan ya sake nanata cewa yana tare da duk wani shiri da zai tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da sake fasalin PDP.
Ya ce yana da cikakkiyar niyyar tallafawa duk wani yunƙuri da zai hana ƙara fadada gibin da ke tsakanin mambobin jam’iyyar.
Gwamna Fintiri ma ya nesanta kansa
A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Adamawa ta hannun Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ta fito fili ta nesanta kanta daga matakin korar Wike ko wasu jiga-jigan PDP.
A wata sanarwa da Fintiri ya wallafa a shafinsa na X, ya ce:
“Ni, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri, Gwamnan jihar Adamawa, ina so in bayyana a fili cewa ban da hannu cikin matsayar korar Ministan FCT, Nyesom Wike daga PDP.”
Gwamna Fintiri ya ce wannan mataki ba zai yi wa jam’iyyar daidai ba, kuma ba zai taba goyon bayan duk wani abu da zai jefa PDP cikin rikice-rikicen da ba su da iyaka ba.

Source: Twitter
“Ina goyon bayan zaman lafiya a PDP” — Fintiri
Ya ce matsayarsa ita ce kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a PDP, yana mai cewa tattaunawa da sulhu su ne hanyoyin da za su ceci jam’iyyar.
Ya kara da cewa:
“Ina kira ga dukkan shugabanni da su yi aiki wajen magance rabuwar kai a cikin jam’iyyar, su kuma yi ƙoƙari wajen ƙirƙirar haɗin kai da kaunar juna.
"A matsayina na ɗan jam’iyya, ina goyon bayan duk wani yunƙuri da zai kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba a PDP.”
Fintiri ya kammala da cewa manufarsa ita ce ganin a samu sulhu da haɗin kai, kuma zai ci gaba da yin aiki don cimma wannan buri.
PDP ta fatattaki Wike, Fayose da wasu
Tun da fari, mun ruwaito cewa, jam’iyyar PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike, tare da wasu daga cikin jiga-jiganta saboda laifuffuka daban-daban.
Daga cikinsi akwai tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da Samuel Anyanwu wanda shi ne tsohon sakataren jam’iyyar.
Chif Olabode George ne ya gabatar da kudirin korar, kuma shugaban PDP na Bauchi, Hon. Samaila Burga, ya mara masa baya a taron jam'iyyar a Ibadan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

