PDP na Dab da Rasa Taraba, Gwamna Ya Bayyana Ranar da Zai Sauya Sheka zuwa APC
- Bayan tsawon lokacin ana magana kan sauya shekarsa, Gwamna Agbu Kefas ya tabbatar da cewa zai koma APC a makon gobe
- Gwamna Kefas ya bayyana cewa zai sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulki a hukumance ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba, 2027
- Majalisar zartarwa ta Taraba ta nuna goyon baya ga gwamnan, ta ce wannan ba tafiya ce da ta shafi duka al'ummar jihar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba, Nigeria - Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya kammala duk wasu shirye-shirya na sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Gwamna Kefas dai na daya daga cikin gwamnonin PDP da ba su halarci babban taron jam'iyyar na kasa da ke gudana a Ibadan, babban birnin jihar Oyo ba.

Source: Facebook
Yaushe gwamnan Taraba zai koma APC?
Tashar Channels tv ta ce yayin da ake maganar rashin halartarsa, gwamnan Taraba ya bayyana cewa zai fita daga PDP tare da shiga APC a hukumance ranar Laraba, 19 ga Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin duba aikin gyaran filin wasa na Jolly Nyame Stadium, iwurin da ake shirin gudanar da bikin sauya shekar tasa a makon gobe.
A cewar Agbu Kefas, wannan mataki da ya dauka na komawa APC ba don wani buri na kansa ba ne, sai don makomar al’ummar Taraba.
Gwamna Kefas ya ce:
“A ranar 19 ga Nuwamba, 2025 zan sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a hukumance. Wannan tafiya ba ta mutum guda ba ce, ta shafi kaddarar al’ummar Jihar Taraba. Mun shirya tarbar manyan baƙi da dama.”
APC ta kafa wa Gwamna Kefas sharadi?
Da aka tambaye shi ko jam’iyyar APC ta gindaya masa sharadi kafin karɓarsa, Gwamna Kefas ya ce jawabin da zai yi a wajen taron zai fayyace komai, ya bar jama’a su yi hukunci da kansu.
A nata bangaren, majalisar zartarwar jihar Taraba ta nuna cikakken goyon bayanta ga gwamnan, ta bakin Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Muslim Aruwa.
A ruwayar Vanguard, kwamishinan ya ce:
“Gwamna shugabannin mu ne. Inda ya nufa, nan muke, ko APC, ko SDP, ko ADC. Wannan mataki na hada inuwa daya da gwamnatin tarayya zai taimaka wajen samar da karin ci gaban jihar, ba don wata bukata ta kashin kai ba.”

Source: Facebook
Muslim Aruwa ya ƙara da cewa wannan tafiya ba ta gwamna kaɗai ba ce, “ta daukacin al’ummar Jihar Taraba ne, kuma muna tare da shi dari biA dari.”
Tsohon gwamnan Abia ya bar PDP
A baya, kun ji labarin cewa tsohon Gwamnan Jihar Abia kuma tsohon Sanata mai wakiltar Abia ta Tsakiya, Sanata Theodore Orji, ya fice daga jam’iyyar PDP.
Sanata Orji wanda ya mulki jihar Abia na tsawon shekaru takwas, ya ce ya yanke shawarar fita daga PDP ne bayan tattaunawa iyalai da abokansa na siyasa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikawa shugaban PDP na Umuahia Ward 1, wacce ta shiga hannun manema labarai ranar Asabar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

