Ana cikin Taron PDP na Kasa a Ibadan, Tsohon Gwamnan Abia Ya Fice daga Jam'iyyar
- Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Theodore Orji ya mika takardar murabus ga shugaban jam'iyyar PDP na mazabar Ummuahia Ward 1
- Sanata Orji wanda ya mulki jihar Abia na tsawon shekaru takwas, ya ce ya yanke shawarar fita daga PDP ne bayan tattaunawa da abokansa
- Wannan na zuwa ne a ranar da jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Ambasada Umar Damagum ta fara babban taro na kasa a Ibadan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Yayin da jam'iyyar PDP ta fara babban taronta na kasa yau Asabar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta kara rasa babban jigo a Kudu maso Gabashin Najeriya.
Tsohon Gwamnan Jihar Abia kuma tsohon Sanata mai wakiltar Abia ta Tsakiya, Sanata Theodore Orji, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP yau Asabar, 15 ga watan Nuwamba, 2025.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikawa shugaban PDP na Umuahia Ward 1, wacce ta shiga hannun manema labarai.
Takaitaccen tarihin siyasar Sanata Orji
Sanata Orji dai ya yi wa’adin mulki biyu watau shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Abia daga 2007 zuwa 2015.
Bayanai sun nuna cewa ya fara hawa mulkin jihar Abia ne a karkashin inuwar jam’iyyar PPA kafin daga bisani ya bar ta ya koma PDP a 2011.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan ya bar YPP zuwa PDP a wancan lokacin sakamakon rikicin siyasa da ya shiga tsakaninsa da wanda ya gada, Orji Uzor Kalu.
Theodore Orji ya yi nasarar lashe wa’adinsa na biyu a 2011 a karkashin PDP, sannan daga baya ya wakilci mazabar Abia ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2023.
A lokacin da rikici ya addabi jam'iyyar a 2024, ɗansa kuma tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Abia, Rt. Hon. Chinedum Orji, ya bar PDP tare da koma wa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan
An samu rudani yayin da PDP ta zabi sabon shugaban jam'iyya na kasa a taron Ibadan
Haka zalika guguwar sauya aheka a wannan lokacin ta hada da matarsa, wacce ta ta rigaya ta fice daga jam’iyyar PDP a bara, cewar rahoton Daily Post.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan Abia ya bar PDP
A cikin wasikar murabus daga PDP da tsohon gwamnan ya rubuta, ya ce:
“Na rubuto muku wannan wasikar ne domin sanar da ficewata daga jam’iyyar PDP daga yau. Wannan matsaya ta biyo bayan tuntuba da tattaunawa da iyalai da abokanai na siyasa.
"Ina godiya da damar da na samu da kuma abubuwan da na koya a lokacin da nake cikin jam’iyyar.”
PDP ta kori Wike da wasu jiga-jigai
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta kori Ministan Abuja, Nyesom Wike, tare da wasu daga cikin jiga-jiganta saboda laifuffuka daban-daban.
Daga cikin wadanda PDP ta sallama daga jam'iyyar gaba daya akwai tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da Samuel Anyanwu wanda shi ne tsohon sakataren jam’iyyar.
Chif Olabode George ne ya gabatar da kudirin korar jiga-jigan a babban taron jam'iyyar da ke gudana a Ibadan, kuma shugaban PDP na Bauchi, Hon. Samaila Burga, ya mara masa baya.
Asali: Legit.ng
