Shugaban NIWA Ya Yi Murabus daga Mukamin da Tinubu Ya Nada Shi, Zai Nemi Takarar Gwamna
- Asiwaju Bola Oyebamiji ya yi murabus daga mukamin shugaban hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya (NIWA)
- Tun a watan Oktoba, 2023, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Oyebamiji a wannan mukami, ya yi shekaru biyu yana jagoranci
- Oyabamiji ya gode wa Shugaba Tinubu da Ministan Harkokin Teku da Tattalin Arzikin Ruwa, Gboyega Oyetola bisa damar da suka ba shi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Kula da Ruwan Cikin Gida ta Kasa (NIWA), Asiwaju Bola Oyebamiji (AMBO), ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Shugaban NIWA ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ne domin mayar da hankali kan burinsa na tsayawa takarar gwamnan Jihar Osun a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Source: Twitter
The Nation ta tattaro cewa Shugaba Tinubu ne ya nada Oyebamiji a matsayin shugaban NIWA a ranar 25 ga watan Oktoba, 2023.

Kara karanta wannan
Ana batun matashin soja da Wike, Tinubu ya yi magana kan jarumtar sojojin Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban hukumar NIWA ya yi murabus
Sai dai a yanzu Oyebamiji, wanda ya kafa tafiyar siyasa a inuwar APC mai suna AMBO, ya ajiye wannan mukami da Tinubu ya ba shi saboda zai fito takarar gwamna a Osun.
Bayanai sun nuna cewa za a gudanar da zaben fidda gwani na APC a ranar 13 ga Disamba, 2025.
Mai magana da yawun tafiyar AMBO, Adebayo Adedeji, ya tabbatar da murabus ɗin Oyebamiji a cikin wata sanarwa da ya rabawa menama labarai ranar Juma'a.
A sanarwar, tsohon shugaban NIWA ya gode wa Shugaba Tinubu da Ministan Harkokin Teku da Tattalin Arzikin Ruwa, Gboyega Oyetola, bisa damar da suka ba shi ya yi wa kasa hidima.
Ci gaba da Oyebamiji ya samar a NIWA
A rahoton Leadership, Adedeji ya ce:
“A cikin shekaru biyu da ya jagoranci NIWA, Oyebamiji ya kafa shugabancina gari, inda ya yi amfani da kwarewarsa ta kusan shekaru 40 a harkokin gwamnati da na ƙasa-ƙasa wajen kawo sabbin tsare-tsare da inganta ayyukan hukumar.”
“A karkashin jagorancinsa, an rage mace-mace da hadurra a kan hanyoyin ruwa na cikin gida da fiye da kashi 70 cikin 100.
"Ya kuma daga kimar wayar da kan jama’a game da tsaron ruwa zuwa wani mataki da ba a taɓa gani ba, tare da inganta walwalar ma’aikata.”
Adedeji ya ce yayin da Oyebamiji ke shirin shiga sabon babi tafiyar siyasar sa, yana da niyyar kawo nagartaccen shugabanci da aikin yi ga al’ummar Jihar Osun.

Source: Twitter
Tinubu ya sabunta nadin Buba Marwa
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake naɗa Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (Mai ritaya) a matsayin shugaban hukumar NDLEA ta kasa.
Wannan na zuwa ne bayan kammala wa’adinsa na farko da ya fara bayan tsohon shugaban ka,Marigayi Muhammadu Buhari ya nada shi a watan Janairu 2021, yanzu zai wuce wa'adi na biyu.
Tun bayan zuwansa NDLEA, ya jagoranci manyan samame da kama mutane sama da 73,000 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da kwace ƙwayoyi daban-daban.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

