Paul Biya Ya Sha Kunya da Ya Biyo Dan Adawan Kamaru Najeriya domin Kama Shi
- Rahotanni sun tabbatar da cewa jagoran 'yan adawa na kasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, yana fake a Najeriya
- Hukumomin Kamaru sun nemi a miƙa musu shi bisa zargin “laifuffuka masu hatsari”, amma Najeriya ta ƙi amincewa
- Lamarin ya faru ne bayan yunƙurin kama shi da wasu jami'an tsaron Kamaru suka yi, kwanaki bayan zaɓen kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gidan jaridu da dama daga yankin Afrika ta Tsakiya sun ruwaito cewa jagoran 'yan adawa na Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, yana Najeriya a garin Yola, jihar Adamawa.
Ya fake a kasar ne bayan da hukumomin Najeriya suka ƙi amincewa da bukatar mayar da shi Kamaru.

Source: Getty Images
Rahoton kafar yada labaran Kamaru ya ce ya taho Najeriya ne bayan yunƙurin kama shi da jami’an tsaron Kamaru suka yi bayan zaben 12, Oktoba, 2025 ya ci tura.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya ta ƙi miƙa Tchiroma ga Kamaru
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar 2, Nuwamba, 2025, wasu jami’an tsaron Kamaru na musamman sun yi yunƙurin kama Tchiroma tare da taimakon wasu jami’an Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan hukumomin kasar Kamaru sun shaida cewa Tchiroma “mai laifi ne mai hatsari”.
Sai dai lokacin da jami’an Najeriya suka tantance shi, suka gane matsayin sa, sai suka ƙi rattaba hannu a kan batun miƙa shi ga hukumomin Kamaru.
Wani rahoto ya ce:
“A yanzu yana ƙarƙashin kulawar jami'an tsaron Najeriya, abin da ya hana duk wani yunƙurin sake kama shi.”
Barazanar gurfanar da Tchiroma a kotu
Kwana guda kafin wannan yunƙuri, ministan harkokin cikin gida na Kamaru, Paul Atanga Nji, ya ce za a gurfanar da Tchiroma kan zargin “tunzura jama’a domin tayar da hankali”.
Ya yi wannan jawabi ne a Yaounde yayin taron manema labarai, inda ya ce Tchiroma ya karya doka ta hanyar bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Source: Getty Images
Wannan gargadi na ministan ya sa ake ganin cewa yunƙurin kama Tchiroma ba shi da nasaba da takardar shari’a kaɗai, har ya shiga fannin siyasar cikin gida ta Kamaru.
Yadda aka so cafke Tchiroma a Kamaru
BBC Hausa ta rahoto cewa an ga sojoji tsakanin huɗu zuwa shida cikin kayan shirin ko-ta-kwana suna sintiri a unguwar Marouare, inda Tchiroma ke zaune.
Sojojin sun kafa wuraren bincike kimanin mita 50 daga gidansa, alamar cewa an nemi toshe duk wata hanyar da zai bi ya fita.
Haka kuma jaridar ta ce wannan ba shi ne karo na farko da ake ƙoƙarin kama shi ba. A ranar zaɓe ma, an tare motar da ke ɗauke da shi, sai dai magoya bayansa suka ƙwace shi.
Tchiroma ya ce ya ci zaben Kamaru
A wani labarin, mun rahoto muku cewa dan adawar Kamaru, Tchiroma Issa Bakary ya yi ikirarin cin zaben shugaban kasar Kamaru.

Kara karanta wannan
Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya
Maganar da dan siyasar ya yi ta tayar da kura lura da cewa hukuma ba ta sanar da sakamako ba a lokacin.
Jam'iyyar shugaba Paul Biya da ya shafe sama da shekara 40 yana mulki a kasar ta yi Allah wadai da kalaman Issa Bakary.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

