Sule Lamido Ya Janye Karar da Ya Kai PDP Kotu? An Ji Magana daga Bakinsa

Sule Lamido Ya Janye Karar da Ya Kai PDP Kotu? An Ji Magana daga Bakinsa

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi tsokaci kan rahoton da ke cewa ya janye karar da ya shigar da jam'iyyar PDP
  • Sule Lamido ya bayyana cewa kotu ta yanke hukunci a shari'ar wanda ya shigar bayan an hana shi yin takarar shugaban PDP na kasa
  • Tsohon gwamnan ya nuna cewa tuni aka mika kwafin hukuncin kotun ga hukumar zabe ta INEC da jam'iyyar PDP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa ya janye karar da ya shigar da jam'iyyar PDP.

Sule Lamido ya nesanta kansa daga rahoton janye karar da yake yi wa PDP tare da bada damar gudanar da babban taron kasa da jam’iyyar ta shirya yi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Sule Lamido ya fadi dalilin shigar da jam'iyyar PDP kara a kotu

Sule Lamido ya magantu kan janye karar da ya kai PDP
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

Lamido ya karyata wannan labari ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin ranar Juma’a, 14 ga watan Nuwamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta hana PDP gudanar da taro

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin karshe na hana PDP gudanar da babban taron kasa da aka tsara yi a ranar Asabar.

Alkalin kotun mai shari'a, Peter Lifu ya yanke hukunci kan karar da Sule Lamido ya shigar.

Me Sule Lamido ya ce janye kara?

Tsohon gwamnan ya bayyana labarin cewa ya janye karar a matsayin karya tsagwaronta.

Ya ce bayan yada wannan rahoto na bogi, ya fara karɓar kiraye-kiraye daga mambobin PDP a faɗin kasar, wadanda suka damu da abin da ke faruwa a wajen taron da aka tsara yi a Ibadan.

“Ina rokon mambobin jam’iyya su lura cewa labarin da aka danganta da ni karya ne."

Kara karanta wannan

Kasa da awanni 24, kotu ta dakatar da babban taron PDP na kasa saboda Sule Lamido

- Sule Lamido

Sule Lamido ya ce babbar kotun tarayya ta yanke hukunci ne da misalin karfe 2:30 na rana, inda ta tabbatar masa da hakkinsa na tsayawa takarar shugabancin PDP, wanda a baya aka hana shi.

Ya kara da cewa kotun ta kuma dakatar da gudanar da taron Ibadan da aka shirya yi a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, har sai jam’iyyar ta bi umarnin kotun.

“Kotun ta kuma hana INEC shiga, saka idanu ko halartar dukkan wani abu da ya shafi taron."

- Sule Lamido

Sule Lamido ya ce bai janye karar da ya kai PDP ba
Sule Lamido wanda ya kai PDP kara kotu Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

Sule Lamido ya bada shawara

Ya bayyana cewa an riga an mika kwafin hukuncin kotun zuwa ga INEC da kuma PDP.

Lamido ya ce ya kamata jama’a su yi watsi da jita-jitar da ke cewa ya janye karar bayan ya gana da Gwamna Seyi Makinde, yana mai cewa labarin ba gaskiya bane.

Ya jaddada cewa yana nan tsayin daka wajen kare hakkinsa a cikin jam’iyyar ta hanyar bin doka.

Kara karanta wannan

Manyan PDP 2 sun ja daga a kan babban taron jam'iyya na kasa

Sule Lamido ya fadi dalilin kai PDP kara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jam'iyyar PDP, Sule Lamid, ya bayyana dalilinsa na shigar da jam'iyyar PDP kara a kotu.

Sule Lamido ya bayyana cewa ya shigar da karar ne domin kwato hakkinsa bayan hana shi yin takarar shugaban PDP na kasa.

Tsohon gwamnan ya ce bai shigar da karar ba don yana fada da jam'iyyar, sai dai don kwato hakkinsa da aka tauye masa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng