Bayan Rabuwa da Kwankwaso, Dan Majalisar Kano, Hon. Koki, Ya Ziyarci Ganduje
- Hon. Sagir Ibrahim Koki ya bayyana jin daɗinsa bayan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje
- Ya ce Ganduje ya tarbe shi da kulawa, ƙauna da shawarwari masu ƙima yayin da ya sanar da canza jam’iyya daga NNPP zuwa APC
- Koki ya ce ya koma APC ne bayan tattaunawa mai zurfi da magoya bayansa kuma manyan jiga-jigan jam’iyyar sun masa tarba mai kyau
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Hon. Sagir Ibrahim Koki, ya yi godiya ga tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Hon. Koki ya bayyana haka ne bayan ziyarar da ya kaiwa Ganduje jim kadan bayan barinsa jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanan da Hon. Koki ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma'a.
Ziyarar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan Koki ya bayyana cewa ya kammala tattaunawar da magoya bayansa, abin da ya kai shi ga ɗaukar matakin komawa jam’iyyar APC.
Dan majalisar Kano ya yabi Ganduje
Koki ya bayyana cewa tarbar da Ganduje ya yi masa ta ƙara masa kwarin guiwa, musamman yadda ya ce tsohon gwamnan Kano ya nuna masa kulawa da goyon baya ba tare da wani sharadi ba.
Bayan ziyartar Ganduje, Hon. Sagir Koki ya rubuta wani saƙo inda ya ce:
“A daren jiya na samu ziyartar ubanmu a matakin kasa da jiha, Dr. Umar Abdullahi Ganduje.
"Kauna da goyon bayansa sun yi mana matuƙar tasiri musamman bayan mun shiga jam’iyyar APC.”
Ya ƙara da cewa:
“Muna matuƙar jin daɗin goyon bayansa, shawarwarinsa da amincewa da ya nuna mana. Wannan abu ne da muke matuƙar godiya a kai.”
Koki ya yi nuni da cewa ziyarar ta ba shi tabbacin cewa sabuwar tafiyarsa a APC za ta kasance mai cike da haɗin kai da kuma ƙarfafa dangantaka da jiga-jigan jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa.

Source: Twitter
Dalilin barin Koki NNPP zuwa APC
A wani saƙon daban da ya wallafa a lokacin da ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC a majalisar wakilai, Koki ce matakin ya biyo bayan tuntuba sosai da ya yi.
Ya ce:
“Bayan tattaunawa mai yawa a mazabata da masoya, na hukunta cewa na koma jam’iyyar APC a matsayin sabuwar jam’iyyata ta siyasa.”
Koki ya bayyana yadda aka karɓe shi a jam’iyyar, yana mai bayyana farin cikin ganawa da manyan shugabannin APC.
Ya ce:
“An karɓe ni cikin girmamawa ta hannun Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, da tsohon shugaban APC na ƙasa, Dr. Umar Ganduje, da Femi Gbajabiamila.
Ya cigaba da lissafa wadanda suka tarbe shi da cewa:
"Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da shugabannin majalisar dattawa, da shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, da manyan APC na Kano.”
Hon Kofa ya koma APC daga NNPP
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan majalisar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya koma jam'iyyar APC.
Hon. Kofa ya sanar da komawa APC ne a wani gagarumin taro da ya shirya tare da magoya bayansa a Kano.
Dan majalisar ya sauya sheka ne wata biyu bayan jam'iyyar NNPP ta sanar da korarsa bisa wasu zarge-zarge da aka masa.
Asali: Legit.ng


