Magana Ta Fito: Sule Lamido Ya Fadi Dalilin Shigar da Jam'iyyar PDP Kara a Kotu

Magana Ta Fito: Sule Lamido Ya Fadi Dalilin Shigar da Jam'iyyar PDP Kara a Kotu

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi tsokaci kan karar da ya kai jam'iyyarsa ta PDP a gaban kotu
  • Sule Lamido ya yi bayanin cewa ba ya kai karar bane don yana rikici da jam'iyyar ko goyon bayan wani bangare
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba zai halarci babban taron jam'iyyar PDP na kasa ba saboda hukuncin da kotu ta yanke

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan karar da ya shigar da jam'iyyar PDP gaban kotu.

Sule Lamido ya bayyana cewa ya kai karar ne domin kawo karshen tauye masa hakkinsa na tsayawa takarar shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Sule Lamido ya fadi dalilin shigar da PDP kara gaban kotu
Sule Lamido da shugaban PDP na kasa, Umar Iliya Damagum Hoto: Muatapha Sule Lamido, Auwal Musa Mohammed Kaska
Source: Facebook

Sule Lamido ya yi wannan bayani ne a ranar Jumma’a yayin hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today tashar Channels TV.

Kara karanta wannan

Kasa da awanni 24, kotu ta dakatar da babban taron PDP na kasa saboda Sule Lamido

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Sule Lamido ya kai karar PDP?

Tsohon gwamnan ya ce ya ce batun ba rikici bane da jam’iyya, illa dai yaki ne na kare mutuncinsa da kimarsa.

"Na je kotu ba don wani mutum ko wani bangare ba, na je ne domin dawo da hakkina da jam’iyyata ta kwace."

- Sule Lamido

Sule Lamido ya kara da cewa batun ya shafi mutuncinsa, darajarsa da martabarsa fiye da komai.

Tsohon gwamnan ya nuna takaicinsa kan halin da PDP ta tsinci kanta, yana mai cewa kauna, haɗin kai da amana da suka kasance a jam’iyyar sun dusashe.

“Na yi nasara a shari’ar, hakan ma yayi kyau amma abin takaici shi ne cewa wannan shari’a ta shafi jam’iyyata ce, ta shafi hadin kanmu, iyalinmu."
“Jam’iyya da ta kasance mai cike da so da amana ta rikide zuwa rigima. Hakan yana sani bakin ciki sosai. Ya kamata a warware matsalar.”

- Sule Lamido

Kara karanta wannan

Manyan PDP 2 sun ja daga a kan babban taron jam'iyya na kasa

Shin Lamido zai janye karar?

Lamido ya ce ba zai iya janye karar ba saboda kotu ta riga ta yanke hukunci, kuma ya kara da cewa ba zai halarci babban taron kasa da aka shirya yi a Ibadan a ranar 15 ga Nuwamba ba.

Sule Lamido ya yi magana kan karar da ya kai PDP
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido Hoto: Sule Lamido
Source: UGC
“A bayyane yake. Ni da kotu ta ceci hakkina, ta bayar da umarnin hana gudanar da taron, ta yaya zan je wurin? Zan je ne in wofintar da abin da na samu daga kotu?”

- Sule Lamido

Ya ce halartar taron zai zama tamkar soke abin da kotu ta tabbatar masa, saboda akwai umarnin kotu na hana taron PDP.

“Ina girmama doka da oda a matsayin cikakken ɗan jam’iyya. Don haka zuwa Ibadan tamkar watsi ne da abin da na samu daga kotu. Kotu ta ce a dakatar da taron. To ta yaya zan je? Ba zan je ba."

- Sule Lamido

Saraki ya ba PDP shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohonn shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ba jam'iyyar PDP shawara.

Kara karanta wannan

PDP ta yi watsi da Wike da mutanensa, ta ce 'babu fashi' kan taronta na Oyo

Saraki ya shawarci jam'iyyar PDP kan kada ta gudanar da babban taronta na kasa da aka shirya gudanarwa a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Tsohon gwamnan ya bukaci PDP da ta kafa kwamitin rikon kwarya wanda zao jagoranci ragamar jam'iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng