Mata 6 da Suka Sha Ƙasa a Zaben Gwamna a Zaɓukan Najeriya

Mata 6 da Suka Sha Ƙasa a Zaben Gwamna a Zaɓukan Najeriya

Wasu mata ‘yan siyasa a Najeriya sun dade suna ƙoƙarin shigaa dama da su ta ɓangaren mulki a siyasar Najeriya.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Bayanan Cibiyar Dimokraɗiyya da Ci gaba (CDD) sun nuna cewa har yanzu ba a taɓa samun mace da ta zama shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa ko zababbiyar gwamna a kasar nan.

Tun daga 1999 har zuwa yau, wakilcin mata a gwamnati bai taɓa kai kashi 10 cikin 100 a matakai daban-daban ba

Aisha Binani, Grace Ifemeludike da wasu matan da suka fadi zaben gwamna a Najeriya
Aisha Dahiru Binani da Chioma Ifemeludike da suka tsaya takarar gwamna a Najeriya Hoto: Aisha Binani support group/Chioma Ifemeludike
Source: Facebook

Legit ta tattaro jerin wasu daga cikin fitattun mata ‘yan siyasa da suka yi tsayuwar daka sosai ko suka kusan lashe zaɓe, amma ƙoƙarinsu bai kai ga nasara ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Aisha Dahiru Binani

Aisha Binani, ita ce mace ta farko da ta kusa doke gwamna mai ci wajen samun nasara a siyasar Najeriya, kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Kara karanta wannan

PPD ta ƙaryata shirin kai wa Matawalle hari, ta gargaɗi APC ta shiga taitayinta

Kotun daukaka kara da ke Abuja ce ta yi watsi da ƙarar da Sanata Aishatu Dahiru Binani ta APC ta shigar, tana kalubalantar nasarar Ahmadu Umaru Fintiri na PDP.

Aisha Binani ta kusa lashe zaben Adamawa
Aisha Dahiru Binani, tsohuwar yar takarar gwamna a Adamawa Hoto: Aisha Dahiru Binani
Source: Facebook

Tun da farko, an samu wasa da hankali bayan rahotanni sun tabbatar da cewa A'isha Binani ke jan gaba a sakamakon zaben jihar a shekarar 2023.

Kotun ta yi hukunci a kan cewa ba ta kawo gamsassun hujjoji ba, kuma ƙarar da ta shigar ba ta cika sharudan doka ba domin an shigar da ita kafin lokacin da doka ta kayyade.

Hakan ya tabbatar da sakamakon zaɓen 18 ga Maris wanda ya bai wa Fintiri nasara a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Adamawa.

2. Chioma Ifemeludike

Chioma Ifemeludike, wacce aka fi sani da IfeDike, ‘yar wasan kwaikwayo ce kuma mai shirya fina-finan Nollywood.

The Cable ta ruwaito cewa ta tsaya takarar gwamna a Anambra ƙarƙashin jam’iyyar AAC a zaɓen da ya wuce, ta taɓa rike matsayin shugabar jam’iyyar a jihar.

Grace Ifemeludike
Chioma Grace Ifemuludike, Yar takarar gwamnan Anambra a 2023 Hoto: Chioma Grace Ifemeludike
Source: Facebook

Ta kammala digiri a Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Anambra, kuma ta ce tana da gogewa tun daga matsayin ‘yar gwagwarmayar ɗalibai da kuma fafutukar kare haƙƙin jama’a.

Kara karanta wannan

ISWAP: Masu hidimar kasa, NYSC sun tsallake rijiya da baya a Borno

Tana da shiri mai farin jini a youtube mai suna Corpers Heaven, kuma tana alfahari da shirya fina-finai a harshen Ibo.

Kamfen ɗinta ya mayar da hankali kan ilimi, tsaro da adalci. Sai dai ana ganin rashin ƙarfin jam’iyyarta a jihar, tare da yadda ake kallon mata a siyasa ya sa ta sha kasa.

3. Ndidi Olieh

Ndidi Olieh, mai shekaru 42, ita ce ‘yar takarar jam’iyyar NRM a zaɓen 2025 da abokin takararta Ogbe Reginald. Ita ce shugabar jam’iyyar a jihar Anambra.

INEC ta tabbatar cewa tana da takardar kammala firamare daga NECO da digiri daga Jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka.

Kamfen ɗinta ya yi niyya kan gyaran tsaro, ilimi da kiwon lafiya a Anambra, tare da neman gabatar da kanta a matsayin sabuwar mafita ga jama'a.

The Peoples Gazette ta ruwaito cewa ƙarancin gogewar siyasa da rashin karɓuwa daga jama’a na daga cikin ƙalubalen da ta fuskanta.

Duk da haka, tsayuwarta takara na kara nuna yadda mata ke ƙara samun ƙarfin guiwa su shiga siyasa a jihar.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

4. Furera Ahmed da Aishatu Mahmud

Furera Ahmed ta jam'iyyar Boot Party (BP) da Aishatu Mahmud ta National Rescue Movement (NRM) su ne mata biyu da suka tsaya takarar gwamnan Kano.

A hirarta da Daily Trust ta wayar tarho, Hajiya Furera ta ce ƙarancin wakilcin mata a siyasar Najeriya shi ne babban dalilin da ya sa mata kamar su ke tsayawa takara.

Ta kuma ce kasancewa mace ‘yar siyasa a irin al’ummar mu ba abu ne mai sauƙi ba,.musamman bayan takararta a shekarar 2023

Ta ce:

"Mutane suna ganin mace da ke siyasa karuwa ce ko tana neman ta wuce mijinta, wanda ba gaskiya ba ne.

Dukkanninsu biyun sun sha kaye a zaɓen.

5. Hadiza Usman

A Zamfara, Hadiza Usman ta Zamfara Labour Party (ZLP) ita ce kaɗai ‘yar takara mace a jerin ‘yan takarar gwamna 14 a zaɓen 2023.

Duk da tsayuwar dakar da ta yi da kamfen ɗin da ya mayar da hankali kan adalci da inganta shugabanci, ita ma ta kasa samun nasara a zaɓen.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun tarwatsa yunkurin sace jami'ansu da limamin addini a Abuja

Ana buƙatar ƙarin mata a siyasa

Barista Halima Abubakar, ɗaya ce daga cikin ƴan ƙungiyar women support group da ke jihar Kano, ta shaida wa Legit cewa ana buƙatar ƙarin mata a siyasa.

Ta ce:

" E gaskiya ne, ana yi wa matan da ke shiga harkokin siyasa, wasu lokutan har fita aiki ma, ana masu kallon karuwai ko marasa kamun kai. Kuma ba gaskiya ba ne."

Halima ta ce suna kira ga gwamnatin da yi hoɓɓasa domin a ware wa mata wasu kujeru wanda su kaɗai za su riƙa takara a kai, domin haɓaka dimokiraɗiyya.

Yar takara a Anambra ta faɗi zaɓe

A baya, mun wallafa cewa fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Chioma Ifemeludike, wadda aka fi sani da IfeDike, ta bayyana godiya ga mutanen da suka zaɓe ta.

IfeDike ta tsaya takarar gwamna ne a ƙarƙashin AAC, kuma ta samu kuri’u 292 kacal daga rumfunan zaɓe 5,718 da aka bude a fadin ƙananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada belin tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, ya fito bayan mako 3 a kurkuku

A maimakon ta nuna bacin rai ko takaicin faduwa zaɓe, jarumar ta zabi ta godewa mutanen da suka zaɓe ta, tare da neman su sa lokaci domin liyafar cin abinci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng