Kasa da Awanni 24, Kotu Ta Dakatar da Babban Taron PDP na Kasa Saboda Sule Lamido
- Yayin da shirye-shiryen taron PDP suka yi nisa, babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta gamsu da hujjojin Sule Lamido
- Mai shari'a Peter Lifu ya umarci INEC ta tsame hannunta daga taron PDP har sai an sanya tsohon gwamnan Jigawa a cikin 'yan takara
- Sule Lamido ya kai kara gaban kotun ne kan hana shi shiga takarar kujerar shugaban PDP na kasa, ya ce hakan ya saba wa doka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigera - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta dakatar da babban taron jam'iyyar PDP na kasa, wanda aka shirya farawa daga gobe Asabar, 15 ga watan Nuwamba, 2025.
Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya watau PDP ta tsara gudanar da babban taron a ranakun Asabar da Lahadi, 15 da 16 ga Nuwamba, 2025 a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Source: Facebook
Kotu ta dakatar da babban taron PDP
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa a hukuncin da mai shari’a Peter Lifu ya yanke yau Juma'a, 14 ga watan Nuwamba, kotun ta kuma dakatar da taron kasa da awanni 24 kafin farawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta dauki wannan mataki ne a karar da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya shigar, yana jalubalantar matakin PDP na hana shi takarar shugaban jam'iyya.
Kotun ta kuma hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sa ido, sa hannu ko kuma amincewa da sakamakon kowanne taron da PDP za ta gudanar ba tare da an haɗa da Sule Lamido, a matsayin ɗan takara ba.
Sule Lamido ya yi nasara kan PDP
Kotun ta ce shaidun da ke gabanta sun nuna cewa an hana tsohon gwamna, Sule Lamido damar karɓar fam ɗin neman takarar kujerar Shugaban Jam’iyyar na ƙasa ba bisa ka’ida ba.
A cewar mai shari'a Peter Lifu, matakin hana tsohon gwamnan damar sayen fom domin tsayawa takara ya saba wa Kundin Tsarin Mulki da Dokokin Jam’iyyar PDP.
Kotu ta bayyana cewa a doka, nauyi ne a kan jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa ’ya’yanta suna samun damar yin aiki ta hanyar samar da yanayi da zai ba su damar cimma burinsu na siyasa.

Source: Twitter
Domin kwato masa hakkinsa, alkalin babbar kotun tarayya ya ce dole a dakatar da duk wani shirin babban taron PDP har sai wanda ke kara ya karbi fam kamar yadda doka ta tanada.
Bugu da kari, ya umarci PDP ta dakatar da taron har sai Sule Lamido ya sayi fam, ya yi yakin neman zabe kuma ya taragoya baya, cewar rahoton The Nation.
PDP ta kafe kan gudanar da taro a Oyo
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi fatali da masu kawo mata tangarda, ta jaddada cewa ba gudu ba ja da baya wajen gudanar taronta na kasa a Ibadan.
Shugaban kwamitin shirya taron jam’iyyar PDP, Gwamna Umaru Fintiri, ya tabbatar da cewa jam’iyyar za ta gudanar da gagarumin taronta a birnin Ibadan kamar yadda aka tsara.
Wannan dai na zuwa ne bayan tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike sun dage wajen ganin taron bai yiwu kamar yadda aka tsara ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


