ADC Ta Yi Mamakin Matakin da Tinubu Ya Dauka bayan Sabanin Wike da A.M Yerima

ADC Ta Yi Mamakin Matakin da Tinubu Ya Dauka bayan Sabanin Wike da A.M Yerima

  • Kakakin jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya soki gwamnatin Tarayya kan shiru da ta yi duk kwanaki biyu da takaddamar Wike da sojan ruwa
  • Bolaji Abdullahi ya ce shiru da gwamnati ta yi na nuna ko dai tana jin tsoron jan kunnen Wike ne, ko kuma tana mara masa baya
  • Ya ce lamarin ya nuna babbar matsalar jagoranci, inda ministoci ke jin za su iya cin zarafin jami’an tsaro ba tare da hukunci ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kakakin jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatin Tarayya ta yi shiru kan takaddamar Nyesom Wike da A.M Yerima.

Bolaji Abdullahi ya ce an shafe kusan awanni 48 bayan wani faifan bidiyo ya nuna Ministan Abuja, Nyesom Wike, yana takaddama da wani jami’in sojan ruwa, Laftanar Yerima, amma har yanzu shiru.

Kara karanta wannan

A.M Yerima: Tsohon jigon APC, Frank ya shawarci Tinubu ya ja kunnen Wike

ADC ta dura a kan Tinubu da Wike kan Yerima
Nyesom Wike, alamar jam'iyyar ADC, A.M Yerima Hoto: Lere Olayinka/ADC Coalition 2023/Isah Ibrahim Suleiman
Source: Twitter

A wani rubutu da ya wallafa a shafin X, Abdullahi ya ce sun jira su ga ko gwamnati za ta fitar da jawabi kan al'amarin zuwa yanzu.

ADC ta dura kan Tinubu

A sakon Bolaji Abdullahi ya ce duk da jiran da su ka yi, amma ba su ga wani bayani daga gwamnatin tarayya a hukumance ba.

Ya ce hakan ya nuna matsalar gwamnati wajen daukar mataki idan lamarin ya shafi manyan mukarrabanta.

Ya ce:

“Shirun gwamnati bayan fiye da awanni 48 yana nuni da cewa ko dai suna tsoron su ci karo da Minista Wike, ko kuma suna goyon bayan yadda ya dauki doka a hannunsa kamar yadda aka gani a bidiyon da ya yadu.”

Bolaji Abdullahi ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin kunya wanda ya kamata ya sa gwamnatin Tarayya ta kira ministan ya yi bayani ko ta ja kunnen sa.

ADC ta yi mamakin sabanin Wike da Soja

Kara karanta wannan

'Ka nemi kashe ni,' Wike ya yi martani mai zafi ga Buratai bayan rigima da soja

Kakakin ADC din ya ce ko da yake cikakkun bayanai game da filin da ake rikici kansa ba su gama fitowa ba, abin mamaki ne ganin Ministan Abuja shi da kansa ya shiga lamarin.

ADC ta yi mamaki da Tinubu ya yi shiri kan batun Wwke
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga/Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

A cewarsa:

“Me ya sa dole sai Ministan Abuja ya shiga aikin tilasta doka kai tsaye? Shin babu hukumomin da ke da alhakin aiwatar da hakan?”
“Me ya sa Minista zai yi wa jami’in soja barazana ko cin mutunci? Wannan ba tsarin gwamnati ba ne.”

Bolaji Abdullahi ya ce lamarin na nuna babbar matsalar jagoranci a cikin gwamnatin Tarayya, inda gwamnati take nuna fifiko ga mukarraban da ta nada maimakon kare dokar kasa.

An shawarci Tinubu kan Wike

A baya, mun wallafa cewa tsohon mataimakin sakataren yada labaran APC, Timi Frank, ya yi kakkausar suka ga Nyesom Wike kan tadammarsa da A.M Yerima a kan wani fili a Abuja.

Ya bukaci shugaba Tinubu ya ja kunnen Wike domin tabbatar da cewa gwamnati na bin doka, tare da tabbatar da mutunta jami'an tsaro da ke sadaukar da rayuwarsu ga kasa.

Ya ƙara da cewa wannan lamari ba wai kawai dalilin rashin jituwa ba ce, amma ya zama alama ta lalacewar tsarin shugabanci a Najeriya da bai kamata a bari ya wuce haka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng