'Yan APC na Neman Yadda za Su Karbe Jihar da PDP ke Mulki

'Yan APC na Neman Yadda za Su Karbe Jihar da PDP ke Mulki

  • Wasu 'yan jam'iyyar APC sun bukaci Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya koma jam’iyyarsu kafin zabukan 2027 domin kowa ya amfana
  • Shugaban 'yan kungiyar APC a Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga ya ce shigar Muftwang APC zai karfafa shiyyarsu
  • Saleh Zazzaga, ya bayyana cewa ra’ayoyin Mutfwang sun dace da falsafar APC da manufofin Shugaba Bola Tinubu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Plateau – Kungiyar APC Arewa ta Tsakiya ta bukaci Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya koma jam’iyyar APC kafin zabukan 2027.

'Kungiyar ta bayyana cewa hakan zai karfafa shugabancin Mutfwang, bunkasa Filato da yankin Arewa ta Tsakiya baki daya.

'Yan APC na zawarcin Caleb Muftwang
Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang Hoto: Caleb Muftwang
Source: Twitter

The Nation ta wallafa cewa Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga, ya bayyana cewa ra’ayoyin Mutfwang sun dace da falsafar APC da manufofin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ganduje, Barau da wasu kusoahi sun dura majalisa da 'yan majalisar NNPP 2 suka koma APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan APC na neman gwamnan Filato

A yayin taron kwanaki na uku na kungiyar APC da aka gudanar a Jos a ranar Alhamis, Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga, ya roki Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang ya dawo APC.

Zazzaga ya ce:

“Gwamna Mutfwang ya nuna cewa shugaba ne mai hangen nesa da ci gaban al’umma. Don cimma burinsa na bunkasa jihar Filato, ya kamata ya bi falsafarsa ta hanyar shiga APC.”

Ya kara da cewa shiga APC zai sanya Mutfwang ya yi aiki kafada da kafada da Shugaba Bola Tinubu wanda ya nuna sha’awa sosai wajen bunkasa Filato.

APC na neman hadin kan Muftwang

Zazzaga ya bayyana cewa mafi yawan ‘yan majalisar Filato suna cikin APC, don haka shiga jam’iyyar zai karfafa hadin kai tsakanin gwamnati da majalisa wajen magance matsalolin tsaro.

Kungiyar ta ce wannan bukata ta fara ne tun bayan zabukan 2023, kuma suna da tabbacin za a samu ci gaba mai dorewa a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Gwamna Caleb ya kammala shirin komawa APC, an ji abin da ya tattauna da Tinubu

Ana fatan sauya shekar Muftwanga za ta taimakawa Filato
Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang Hoto: Caleb Muftwang
Source: Twitter

Zazzaga ya kuma bayyana wasu nasarorin kungiyar, ciki har da kafa hukumar ci gaban yankin Arewa ta Tsakiya.

Duk da cewa wasu ‘yan APC sun nuna rashin goyon baya ga yiwuwar sauya sheka, Zazzaga ya musanta wannan ra’ayi, yana mai cewa:

Ya ce:

“Siyasa na bukatar lokaci, hangen nesa da daidaituwa. Lokaci ya yi da Mutfwang ya shiga APC domin hada karfinsa da jam'iyya mai ci ta APC.”

'Dan majalisa ya koma APC

A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar APC ta samu ƙarin 'yan a Majalisar Wakilan Tarayya, lamarin da ya ƙara mata ƙarfin siyasa a daidai lokacin da ake dab da fara takaddamar siyasar 2027.

Shugaban Kwamitin Harkokin Gida na Majalisar Wakilai, Hon. Daniel Amos, ya sauya sheƙa daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa APC mai mulki a kasar nan karkasin Bola Tinubu,

Hon. Amos, wanda ke wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a Jihar Kaduna, ya fara bayyana matakin nasa ne a wani taro da aka gudanar a filin wasa na Kafanchan, inda ya ce ya bar PDP.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2025: Abubuwa 7 da suka taimaka wa Gwamna Soludo ya doke APC, PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng