PDP Ta Yi Watsi da Wike da Mutanensa, Ta Ce 'Babu Fashi' kan Taronta na Oyo
- Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce PDP ta kammala shirin zuwa Ibadan don taron kasa da ta shirya gudanarwa
- Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar sun fara isa jihar Oyo da za a gudanar da taron
- A Rivers da Nyesom Wike ya fito, jam’iyyar ta rabu gida biyu kan halartar taron saboda sabanin umarnin da kotu ta bayar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Shugaban kwamitin shirya taron jam’iyyar PDP, Gwamna Umaru Fintiri, ya tabbatar da cewa jam’iyyar za ta gudanar da gagarumin taronta a birnin Ibadan kamar yadda aka tsara.
Sanarwar ta fito ne a wata gajeriyar hira da gwamnan ya yi da manema labarai a ranar Alhamis da daddare.

Source: Original
Hadimin gwamnan Adamawa, Paul Barnabas ya tabbatar da cewa taron zai gudana a wani sako da ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan PDP sun yi taro a Abuja
Manyan PDP sun yi taro a gidan gwamnatin Bauchi da ke Asokoro, inda manyan jiga-jigan jam’iyyar suka hallara.
Cikin wadanda suka hallara akwai gwamnan Oyo, Seyi Makinde, shugaban PDP na kasa, Umar Damagum, tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.
Kakakin jam’iyyar, Debo Ologunagba, da kuma tsohon ministan Najeriya, Tanimu Turaki duk sun hallara taron.
Bayan fitowarsu daga taron, Fintiri cikin annashuwa ya ce:
“Mun fito daga taron jiga-jigan jam’iyya inda aka yanke matsaya. Ina sanar da ku a nan cewa za mu tafi Ibadan domin gudanar da taronmu, kuma taron nan wajibi ne, babu canjawa.”
Shirye-shiryen PDP domin taro a Oyo
Fintiri bai yi karin bayani kan wasu batutuwa ba domin jami'in tsaro ya ja shi ya bar wurin bayan amsa tambayoyi kaɗan.
Wannan ya bayyana cewa jam’iyyar ta yanke shawarar kammala dukkan shirye-shirye ba tare da wani jinkiri ba, duk da kalaman masu adawa ko matsalolin da ke tunkaro jam’iyyar a wasu jihohi.
Duk da haka, gwamnatin Adamawa ta tabbatar da cewa za a yi taron ne a a ranakun Asabar da Lahadi, 15 da 16 ga Nuwamban 2025 da karfe 10:00 na safe.
Rahotanni sun nuna cewa taron zai gudana ne a filin wasan Lekan Salami, a Adamasingba, a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Mutanen Wike za su ki zuwa taron PDP
A Jihar Rivers da ministan Abuja, Nyesom Wike ya fito, PDP ta kasu gida biyu kan batun halartar taron.

Source: Facebook
Shugaban wani bangare na jam’iyyar a jihar, Robinson Ewor, ya tabbatar da cewa su za su je Ibadan.
Sai dai bangaren da ke goyon bayan Nyesom Wike ya dauki matsaya ta daban domin kauracewa taron.
Mai magana da yawun wannan bangare, Kenneth Yorwika, ya ce su ba za su je taron ba saboda umarnin kotu.
A cewarsa:
“Mun samu hukuncin Babbar Kotun Tarayya daga Mai Shari’a Omotosho da ta dakatar da taron. Ta yaya za mu halarta?”
Saraki ya nemi daga taron PDP
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya yi magana kan taron PDP da ake shirin yi.
Bukola Saraki ya bukaci a daga taron domin neman hanyar da za a warware rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP.
Rikici ya mamaye jam'iyyar PDP tun gabanin zaben 2023 wanda har yanzu ba a samu hanyar shawo kan matsalar ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


