'Yan Majalisar NNPP 13 Na Shirin Sauya Sheka daga Jam'iyyar? An Ji Gaskiyar Zance

'Yan Majalisar NNPP 13 Na Shirin Sauya Sheka daga Jam'iyyar? An Ji Gaskiyar Zance

  • An yada wata jita-jita mai cewa wasu 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar NNPP sun shirya sauya sheka zuwa wasu jam'iyyu daban
  • 'Yan majalisar wakilan masu alaka da tafiyar Kwankwasiyya sun fito sun yi bayani kan jita-jitar da aka yada a kansu kan sauya sheka
  • Kalaman na su dai na zuwa ne bayan wasu 'yan majalisar NNPP guda biyu daga jihar Kano sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - ‘Yan majalisar wakilai da aka zaba a jam'iyyar NNPP sun yi martani kan batun suna shirin sauya sheka zuwa jam'iyyu.

'Yan majalisar na NNPP sun nesanta kansu daga jita-jitar da ke yawo cewa suna shirin sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu.

'Yan majalisar NNPP sun musanta shirin sauya sheka
'Yan majalisar wakilai yayin zaman majalisa Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce 'yan majalisar 13 sun bayyana matsayarsu ne a taron manema labarai da Hon. Garba Diso ya jagoranta a Abuja a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Lakurawa sun kai harin ta'addanci a Sokoto, sun yi barna mai girma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan bayani ya zo ne bayan ‘yan majalisa biyu na NNPP daga Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin da Hon. Sagir Koki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a yayin zaman majalisar wakilai na ranar Alhamis.

Me 'yan NNPP suka ce kan ficewa daga cikinta?

'Yan majalisar wadanda ake dangantawa da tafiyar Kwankwasiya a jihar Kano, sun tabbatar da cikakkiyar biyayyarsu ga NNPP da jagorancinta mai hangen nesa.

Da yake magana da manema labarai, Diso ya bayyana rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa “’yan majalisar Kwankwasiya suna shirin sauya sheka” a matsayin tsantsagwaron karya.

“Muna son mu karyata wadannan jita-jita marasa tushe, kuma muna rokon jama’a da masoyan NNPP da ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su yi watsi da irin wadannan bayanai na bogi."

- Hon. Garba Diso

Su wa ke yada jita-jita kan 'yan NNPP?

Ya ce wadannan jita-jita wani shiri ne na makiyansu a siyasa da ke jin tsoron karfin jam’iyyar NNPP da karuwar tasirin Kwankwasiya musamman a Kano da Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Ganduje, Barau da wasu kusoahi sun dura majalisa da 'yan majalisar NNPP 2 suka koma APC

'Yan majalisar NNPP sun musanta shirin barin jam'iyyar
Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook
“A matsayinmu na ‘yan majalisa, aikinmu na kundin tsarin mulki shi ne yin aiki tare da takwarorinmu na sauran jam’iyyu domin ci gaban kasa."
"Tatttaunawa da sauran ‘yan siyasa ba yana nufin rashin biyayya ba ne, kuma ba alamar sauya sheka ba ne."
“Mun tsaya kan biyayyar mu ga NNPP da ra’ayin Kwankwasiya wanda ke fafutukar adalci, daidaito da hada kai. Babu wata farfaganda da za ta girgiza wannan akida."
“Mun tsaya tsayin daka, mun hada kai kuma muna da cikakkiyar biyayya ga NNPP, ga tafiyar Kwankwasiya, da al’ummar da muke wakilta."

- Hon. Garba Diso

'Yan APC sun koma NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mambobin jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano sun sauya sheka zuwa NNPP mai mulki.

Mambobin na APC wadanda adadinsu ya kai sama da 50, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP a karamar hukumar Kibiya ta jihar Kano.

Masu sauya shekar sun bayyana cewa sun fice daga APC saboda rashin tsinana masu komai a yankin a shekarun da ta kwashe kan madafun iko.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng