Ganduje, Barau da Wasu Kusoshi Sun Dura Majalisa da Yan Majalisar NNPP 2 Suka Koma APC
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kara yawan 'yan majalisar da take da su a majalisar wakilan Najeriya
- 'Yan majalisa guda biyu na jam'iyyar NNPP daga jihar Kano sun sauya sheka zuwa APC a gaban manyan 'yan siyasa
- Abdullahi Umar Ganduje, shugaban APC na kasa da manyan kusoshin jam'iyyar aun halarci majalisar don ganin sauya shekar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - ‘Yan majalisar wakilai biyu daga jihar Kano, Sagir Koki da Abdulmumin Jibrin sun sauya sheka daga jam'iyyar NNPP.
'Yan majalisar wakilan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ce an bayyana sauyin shekarsu ne a hukumance a ranar Laraba lokacin da shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, ya karanta wasikun da kowannensu ya aike wa majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa 'yan NNPP suka koma APC?
A cikin wasikunsu, ‘yan majalisan sun bayyana cewa sun yanke shawarar barin NNPP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka addabe ta, rahoton Leadership ya tabbatar da labarin.
Sun kuma kafa hujja da rashin haɗin kai, da kuma rarrabuwar kawuna da ba za a iya sulhuntawa ba a matakin jiha da na kasa, a matsayin dalilinsu na ficewa daga jam'iyyar.
Wani bangare na wasikar na cewa:
“Wadannan rikice-rikice da suka daɗe suna faruwa sun haifar da yanayi da bai dace da ci gaba da yin siyasa ko kare muradun al’ummata ba."
Sun kara da cewa bayan tattaunawa da al’ummominsu, abokan siyasa, da masu ruwa da tsaki, sun yanke shawarar cewa shiga APC zai ba su damar ci gaba da wakilci mai inganci da bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa.
Ganduje da kusoshin APC sun je majalisa
Kafin sanarwar, majalisar ta soke wasu dokokinta na cikin gida domin karɓar tawagar shugabannin APC daga Kano da wasu baki na musamman daga majalisar dattawa.
Tawagar ta haɗa da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele, babban mai tsawatarwa,, Tahir Monguno, shugana marasa rinjaye, Osita Ngwu da kuma Ibrahim Ashiru, da sauransu.

Kara karanta wannan
Ba sauki: Jiragen yakin sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda a jihohin Arewa 3
Haka kuma, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, da tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullahi Ganduje, sun halarci zaman tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Source: Twitter
Bayan karanta wasikun, shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya taya su murna da cewa:
“Ina taya ku murna da dawowa cikin babbar jam’iyya mafi girma a Afirka.”
A yayin sanarwar, shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Kingsley Chinda, ya yi kokarin kalubalantar sauyin shekan, amma shugaban majalisar bai amince da bukatarsa ba.
Daga nan, wasu ‘yan APC da sababbin masu sauya sheka suka tashi zuwa gaban kujerar shugaban majalisar domin musabaha da daukar hoto.
A cikin barkwanci, shugaban majalisar ya juya zuwa ga Hon. Chinda ya ce: “Hon. Chinda, zo ka haɗu da mu." Wannan barkwanci ya sa an yi dariya sosai a zauren majalisar.
'Yan APC sun koma NNPP a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu koma baya a siyasar jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yamma.
Kwamishinan ma’aikatar jin kai da rage talauci na jihar Kano, Alhaji Adamu Kibiya, ya karbi mambobin jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa NNPP.

Kara karanta wannan
Kebbi: Mataimakin shugaban majalisa ya kubuta daga hannun 'yan bindiga, an ji yadda ya tsira
Kwamishinan ya karbi mambobin ne sama da 50 daga gundumar Kibiya da ke cikin karamar hukumar Kibiya, waɗanda suka bar APC zuwa NNPP.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
