Kwankwaso da Ganduje Sun Manta da Gabar Siyasa, An Yi Wasa da Dariya da aka Hadu

Kwankwaso da Ganduje Sun Manta da Gabar Siyasa, An Yi Wasa da Dariya da aka Hadu

  • Tsofaffin gwamnonin Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje sun hadu karo na farko tun bayan zaben 2023
  • Tsofaffin shugabannin biyu masu zafin adawa da juna sun hadu a gidan tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Ahmad Adamu Mu’azu, a Abuja
  • Jama’a da dama sun bayyana mamaki da fatan sulhu tsakanin manyan shugabannin siyasar Kano da hanyar yanzu ke adawa da junansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsofaffin gwamnonin Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun hadu karo na farko tun bayan kammala zaben 2023.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi haduwa ne a gidan tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu, da ke Abuja, inda suka je domin yin ta’aziyya bisa rasuwar mahaifiyarsa.

Kara karanta wannan

Hotunan Abba Kabir da Ganduje sun yi kicibis a karon farko tun bayan zaben 2023, sun yi gaisuwa

Kwankwaso da Ganduje sun hadu a Abuja
Hoton Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Gnaduje a gidan Ahmad Adamu Mu'azu Hoto: A Fayyace
Source: Facebook

Wani faifan bidiyo da Premier radio ta wallafa a shafinta na Facebook ya nuna yadda jagororin biyu suka gaisa, ana murna ana raha, kafin Kwankwaso ya zauna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso da Ganduje sun hadu

Jaridar Solcebase ta ruwaito cewa haduwa shugabannin ta zo da mamaki ga mutane da dama, musamman bayan an yi la’akari da tsawon lokacin da aka samu rikici da sabani a tsakaninsu.

Masu lura da harkokin siyasa sun ce wannan na iya zama sabon babi a dangantakarsu, musamman ganin yadda suka yi musayar gaisuwa cikin natsuwa da mutuntaka.

Da farko dai Ganduje ne ya mika wa Kwankwaso hannu yana murmushi, shi ma jagoran Kwankwasiyya ya karba ba tare da nuna alamar wata matsala a fuskarsa ba.

Bayan an gaisa, an yi raha da dariya kuma sai Sanata Kwankwaso ya zauna, yayin da Ganduje ya ci gaba da gaisawa da mutanen da ke wurin.

Ra'ayin jama'a kan haduwar Kwankwaso da Ganduje

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi kazamin karo a Borno, an kashe mayakan ISWAP 50

Wasu daga cikin ‘yan siyasa da masoya daga Kano sun nuna farin ciki da wannan ganawa, suna fatan ta kawo karshen rikicin da ya daɗe yana janyo rabuwar kai tsakanin iyayen siyasar Kano.

Masu bibiyar bidiyon da aka wallafa a shafin Facebook na gidan rediyon sun kuma bayyana yadda zafin adawa ga magoya baya ba za ta amfana masu komai ba.

An gaisa a tsakanin Kwankwaso da Ganduje
Hotun Kwankwaso da Ganduje a yayin haduwarsu a Abuja Hoto: Auwalu Yunusa Ajingi
Source: Facebook

ail Captain ya wallafa cewa:

“Yau dai burin Kwankwaso ya cika, ya hadu da mai gidan sa a siyasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje.”

Fauziyya Usman ta ce:

“Wato a harkar nan Malam talaka shi yake wahalar da kansa 🤷.”

Muhammad Bello Alkasim cewa ya yi:

“Nai farin ciki da haduwar nan, Allah ya daidaita tsakaninsu, albarkar Annabi Muhammadu (SAW).”

Shi ma Rijiyar_lemo City ya bayyana cewa:

“Su fa daga nesa ne kawai suke rigima saboda mafutarsu.”

Yusuf Ibn Shitu ya kara da cewa:

“Tsakaninku da masoyanku Allah ya saka musu, kun cuce su, kun raba su da ‘yan uwansu saboda soyayyar da suke muku, ashe ku ma a hade ku ke.”

Haduwar Kwankwaso da tsohon shugaban APC, ta zo ne kwana guda bayan Ganduje ya hadu da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

Kara karanta wannan

Abubuwa 8 da ba ku sani ba game da jihar Anambra da ake shirin zaben gwamna

Ganduje ya hadu da Abba a Kano

A baya, mun wallafa cewa gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun hadu karo na farko tun bayan kammala zaben 2023.

Rahotanni sun tabbatar da cewa haduwar ta faru ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda shugabannin biyu suka yi musayar gaisuwa cikin natsuwa da murmushi a fuskokinsu.

Wannan ne karo na farko da suke ganin juna a zahiri tun bayan babban zaben 2023 wanda ya haifar da rikici da kai-komo har zuwa kotu, kafin daga bisani a tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng