PDP Ta Bayyana Makomar Babban Taronta na Kasa bayan Hukuncin Kotu
- Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja, ta dakatar da jam'iyyar PDP daga gudanar da babban taronta na kasa
- Jam'iyyar PDP ta mayar da martani kan umarnin kotun, inda ta nuna cewa ko kadan ba za ta yi biyayya gare shi ba
- PDP mai adawa ta yi nuni da wani hukuncin kotun koli wanda ya ba jam'iyyu hurumin tafiyar da harkokinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta sha alwashin ci gaba da shirin gudanar da babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranakun 15 da 16 ga Nuwamban 2025.
Jam'iyyar PDP ta sha alwashin ne duk da sabon umarnin babbar kotun tarayya da ya hana ta yin hakan.

Source: Twitter
PDP ta sha alwashi kan babban taronta
Mataimakin sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar PDP, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana hakan ga jaridar Daily Trust.
Ibrahim Abdullahi ya ce sabon umarnin kotu da ya dakatar da taron bata lokaci ne kawai.
Ya jaddada cewa jam'iyyar na bin wani hukuncin Kotun Koli wanda ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa suke da hakkin gudanar da harkokinsu na cikin gida.
An hana PDP gudanar da taro
Maganganun Ibrahim Abdullahi sun biyo bayan hukuncin da alkalin babbar kotun tarayya, mai shari'a, Peter Lifu, ya bayar a Abuja a ranar Talata, inda ya hana PDP gudanar da taron.
Wannan umarni ya saba wa hukuncin babbar kotun jihar Oyo, wacce ta ba jam'iyyar damar ci gaba da shirye-shiryen.
PDP ta ce ba gudu ba ja da baya
A martanin da ya yi, Ibrahim Abdullahi yace jam'iyyar ba za ta bari 'hukuncin da aka sayo' ya yi tasiri a kanta ba, inda ya kara da cewa PDP jam'iyya ce ta 'yan Najeriya ba ta kotu ba.

Source: Twitter
“Wannan hukuncin bata lokaci ne kawai. Mun riga mun wuce matakin da za a iya hana mu ci gaba."
"Mu ba jam'iyya ba ce da kotu ta kirkira ba, mun kasance jam'iyyar 'yan Najeriya, kuma ya kamata mu saurari ra'ayin 'yan Najeriya, ba hukuncin da aka sayo ba."
“Ba za su hana mu ba. Muna da hukunci na Kotun Koli da ke cewa ikon gudanar da harkokin cikin gida na jam'iyyun siyasa na hannunsu su kaɗai, kuma muna bin wannan hukunci."
“Ko da wani zai yi watsi da umarnin babbar kotun jihar Oyo da ya ba mu izini, ba za a iya watsi da hukuncin Kotun Koli ba."
"Ba za mu bari a ci gaba da gwara mana kai da hukuncin kotu masu cin karo da juna ba. Mun yi nisa, ba za a iya dakatar da mu ba.
“Su jira. Idan mun kammala, idan sun ga dama su ce ba za su amince da shi ba. Koma dai menene, za su iya ɗaukaka kara, amma mu za mu ci gaba shirinmu."

Kara karanta wannan
Zargin ta'addanci: Kotun tarayya ta saka ranar yanke hukunci a kan shari'ar Nnamdi Kanu
- Ibrahim Abdullahi
Sanatan PDP ya koma APC
A wani labarin kuma kun ji cewa sanata mai wakiltar Cross River ta Arewa, Agom Jrigbe, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Santa Jarigbe Jarigbe ya bayyana rikice-rikicen cikin gida a PDP wanda ya ke ganin ba za a iya kawo karshensu ba a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar.
Hakazalika ya bayyana cewa bayyana cewa APC ta ba shi dandalin da zai ci gaba da wakiltar mazabarsa da kwanciyar hankali da gaskiya wajen kawo ci gaba.
Asali: Legit.ng

