Gwamna Caleb Ya Kammala Shirin Komawa APC, an Ji Abin da Ya Tattauna da Tinubu

Gwamna Caleb Ya Kammala Shirin Komawa APC, an Ji Abin da Ya Tattauna da Tinubu

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya na ci gaba da fuskantar matsaloli yayin take rasa jiga-jiganta zuwa APC mai mulki
  • Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya
  • Sai dai wasu magoya bayansa sun soki matakin, suna zargin tsohon gwamna Joshua Dariye da shugabannin APC da kokarin jawo shi ta bayan fage

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa Gwamna Caleb Mutfwang yana daf da barin jam'iyyar PDP mai adawa.

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, na iya barin PDP a kowane lokaci domin komawa jam’iyyar APC, kamar yadda wasu makusanta suka tabbatar.

Gwamna Caleb ya gama shirin komawa APC
Gwamna Caleb Muftwang da Bola Tinubu. Hoto: Caleb Mutfwang, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Gwamn ya gana da wasu kan komawa APC

Rahoton The Guardian ya ce Mutfwang, wanda ya hau mulki karkashin PDP bayan cin zaben 2023 ya ce bai yi shawara da jama’a sosai ba kafin matakin.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ya bayyana cewa ya sanar da tsohon gwamna Jonah Jang da wasu kalilan, inda ake cewa Jang bai yi masa alkawarin nasara ba a sabuwar jam’iyya.

Wasu na kusa da Mutfwang sun ce shugaban kasa ne da kansa ya gayyace shi domin su hada kai wajen bunkasa jihar da kasa baki daya.

A cewar wasu, wannan shawarar ta tayar da kura a jam’iyyar APC, musamman tsakanin bangaren tsohon gwamna Simon Lalong da na shugaban jam’iyyar Nentawe Yilwatda.

Gwamna Caleb zai koma APC nan ba da jimawa ba
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Source: Facebook

Matsalar da Gwamna Caleb zai fuskanta

Wasu magoya bayan Gwamna Mutfwang daga PDP sun bayyana rashin jin dadinsu, suna cewa hakan ya sabawa yarjejeniyar da suka yi da shi tun zaben 2023.

Sun zargi tsohon gwamna Joshua Dariye da shugaban APC na jihar, Rufus Bature, da kokarin shigar da gwamnan jam’iyyar ta bayan fage kuma ta hannun mataimakin shugaban kasa.

Wasu sun gargadi gwamnan da ka da ya mika ragamar PDP, suna cewa akwai wasu da ke son amfani da shi don karbe shugabancin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Matakin da jam'iyyar PDP ke shirin dauka kan Nyesom Wike

Jigon PDP ya kalubalanci Gwamna Caleb

Haka kuma, wani jigo a PDP ya tambayi Mutfwang dalilin da yasa zai yi watsi da mutanen da suka yi masa addu’a har ya lashe zabe.

Gwamnan dai bai ba da amsa kai tsaye ba, yayin da magoya bayansa ke ganin cewa shawarar tasa ita ce mafi alheri ga jihar Plateau.

A wannan shekara ta 2025, gwamnonin jam'iyyun adawa da dama sun yi watsi da su domin shiga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya saboda ci gaba da inganta jihohinsu.

Gwamnoni 4 za su bar jam'iyyunsu - APC

Mun ba ku labarin cewa akwai yiwuwar wasu gwamnonin jihohi hudu a Arewa da Kudancin Najeriya za su bar jam'iyyun adawa zuwa APC kafin karshen 2025.

Mataimakin shugaban APC na kasa (Kudu maso Gabas), Dr. Ijeoma Arodiogbu ya ce tattaunawa da gwamnonin ta kai matakin karshe domin komawa jam'iyyar.

Daga cikin gwamnonin da ya ambaci sunayensu akwai Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato da Gwamna Simi Fubara na Rivers.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.