Sanata PDP Ya Jefar da Jam’iyya Mai Adawa, Ya Fadi Amfanin da APC Za Ta Yi Masa
- Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sake rashin Sanata a majalisar dattawa bayan ya yanke shawarar watsar da ita
- Sanatan ya ce APC na da dandalin ci gaba da kwanciyar hankali da zai ba shi damar wakiltar mazabarsa yadda ya kamata a majalisar dattawa
- Sauya shekar tasa na zuwa ne yayin da PDP ke fama da rikicin shugabanci tsakanin magoya bayan Umar Damagum da na Nyesom Wike
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Majalisar dattawa a Najeriya ta sake sanar da ficewar wani sanata daga jam'iyyar PDP mai adawa wanda ya koma APC.
Sanata Agom Jarigbe, mai wakiltar mazabar Cross River ta Arewa, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Source: Twitter
Sanatan PDP ya fadi dalilin shiga APC
A cewar rahoton NASSTV da aka wallafa a YouTube, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ne ya karanta wasikar a ranar Talata 11 ga watan Nuwambar 2025.
Majiyoyi suka ce Jarigbe ya bayyana rikice-rikicen cikin gida a PDP a matsayin dalili wanda ya ke ganin ba za a iya kawo karshensu ba.
Jarigbe ya ce:
“Na rubuta wasika ne domin sanar da ficewata daga jam’iyyar PDP wacce ta daukaka ni zuwa majalisar dattawa domin wakiltar mutanen Cross River ta Arewa.
“Na yanke wannan hukunci bayan tunani mai zurfi kan halin da jam’iyyata ta tsinci kanta, inda rikice-rikice suka zama ruwan dare.”
Jarigbe ya bayyana cewa APC ta ba shi dandalin da zai ci gaba da wakiltar mazabarsa da kwanciyar hankali da gaskiya wajen kawo ci gaba.
A cewarsa:
“A bisa hakan, na yanke shawarar shiga jam’iyyar APC a karkashin shugabancin Bola Tinubu domin samun ingantaccen wakilci da ci gaban mazabata.”

Source: Facebook
Abin da Barau ya fadawa Sanata Jarigbe
Barau Jibrin ya tarbe shi da murna a majalisa, inda ya ce suna maraba da shi a cikin jam'iyyar APC domin ba da tashi gudunmawa.
Barau ya ce:
“Muna maraba da kai cikin jam’iyya mai ci gaba."
Sauya shekar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da PDP ke cikin rikicin shugabanci da ya raba jam’iyyar gida biyu, kowanne bangare yana dakatar da dayan.
Rahoton Punch ya ce rikicin ya kara kamari ne bayan kotun tarayya ta hana gudanar da taron kasa na PDP da aka shirya a Ibadan, Oyo, ranar 15 ga Nuwamba.
Rikicin ya fi tsanani tsakanin magoya bayan mukaddashin shugaban jam’iyya Umar Damagum da bangaren Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
PDP za ta dauki mataki kan Wike
Mun ba ku labarin cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, na ci gaba da zama karfen kafa ga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Jam'iyyar PDP ta shirya daukar matakin ladabtarwa kan Wike wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Rivers a Kudancin Najeriya.
Shirye-shiryen daukar matakin dai na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke shirin gudanar da babban taronta na kasa a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Asali: Legit.ng

