NNPP Ta Zargi Kwankwaso da Cin Amanar Jam'iyya, an Ambaci Laifuffukansa
- Tsagin NNPP ya ce Rabiu Kwankwaso ne ya jawo ficewar Abdulmumin Jibrin zuwa APC da Oluremi Oguntoyinbo zuwa PDP
- Sakataren tsagin NNPP, Ogini Olaposi, ya zargi Kwankwaso da aikata abin da ya kira “cin amanar jam’iyya” da kokarin karbe shugabanci
- Ya ce rikicin shugabanci da ke tsakanin Kwankwaso da wasu jiga-jigai na jam’iyyar ne ya janyo 'yan siyasa na sauya sheka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsagin jam’iyyar NNPP ya daura alhakin ficewar wasu manyan ‘ya’yanta zuwa APC da PDP a kan tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Jam’iyyar ta bayyana cewa, abin da ya jawo wadannan sauye-sauyen jam’iyya shi ne rashin daidaito da rikicin cikin gida da Kwankwaso da magoya bayansa suka haddasa.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa sakataren tsagin jam’iyyar na kasa, Dr Ogini Olaposi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Ya yi magana yana mai cewa wannan matsala ta samo asali daga yadda Kwankwaso ke kokarin mamaye jam’iyyar da tafiyarsa ta Kwankwasiyya.
NNPP ta zargi Kwankwaso da cin amana
Dr Olaniyi ya bayyana cewa jam’iyyar ta shiga cikin rikice-rikicen shari’a da na cikin gida tun bayan da Kwankwaso da magoya bayansa suka yi yunkurin karbe shugabancin NNPP.
A cewarsa:
“Babu dan siyasa mai hankali da zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar da mutum daya ke ganin kansa a matsayin mai yanke duk wata shawara.”
Ya kara da cewa wannan hali na Kwankwaso ya sa mutane da dama a Kano da sauran jihohi sun bar jam’iyyar don komawa APC ko PDP, inda suke ganin za su samu dama da kwanciyar hankali.
Jibrin da Oguntoyinbo sun girgiza NNPP
A cikin makon nan Abdulmumin Jibrin, ya koma jam’iyyar APC tare da bayyana goyon bayansa ga sake takarar shugaba Bola Tinubu a 2027.

Source: Twitter
Haka kuma, tsohon dan takarar gwamnan NNPP a Ogun, Ambasada Oluremi Oguntoyinbo, ya fice daga jam’iyyar tare da shiga PDP.
Olaposi ya bayyana cewa wadannan matakai ba abin mamaki ba ne domin jam’iyyar na fuskantar matsin lamba daga ‘yan cikin gida masu neman kare muradunsu.
Daily Post ta wallafa cewa Olaposi ya ce:
“Kwankwaso da magoya bayansa sun ci amanar Dr. Boniface Aniebonam, wanda shi ne wanda ya kafa NNPP, kuma ya ba Kwankwaso damar yin takarar shugaban kasa ba tare da wani sharaɗi ba,”
Inji shi.
NNPP ta yi magana kan sauya sheka
Olaposi ya ce NNPP ba ta da wata matsala da wadanda suka yanke shawarar barin jam’iyyar, domin ‘yancin kowane dan kasa ne ya zaɓi jam’iyyar da yake so.
“A siyasarmu, babu dole. Duk wanda bai yarda da manufofin NNPP ba, yana da ‘yanci ya tafi, kamar yadda masu sha’awar manufofin mu ke da ‘yanci su shiga,”
Inji shi.
Ya kara da cewa NNPP ba ta da niyyar yin siyasar tilas, kuma jam’iyyar na alfahari da tsayawa kan gaskiya da rikon amana a fagen siyasa.
Hon. Kofa ya koma APC a jihar Kano
A wani rahoton, mun kawo muku cewa bayan wata biyu da korarsa daga jam'iyyar NNPP, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya koma APC.
Hon. Kofa ya koma APC ne a wani gagarumin taron da ya shirya tare da magoya bayansa na Kiru da Bebeji.
Dan majalisar ya ce ya tara dubban magoya bayansa ne domin kaucewa abin da ya faru a baya na cewa shi daya ya koma APC.
Asali: Legit.ng


