Zaben Anambra: Dan Takarar LP Ya Bayyana Abin da Ya Hana Shi Lashe Kujerar Gwamna
- Dan takarar jam'iyyar LP a zaben gwamnan jihar Anambra, George Moghalu, ya yi tsokaci kan rashin nasarar da ya yi
- George Moghalu ya koka da cewa ba a gudanar da sahihin zabe ba a zaben na ranar, Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025
- Hakazalika ya bayyana dalilinn da ya sanya gaza lashe rumfar zabensa wadda Gwamna Chukwuma Soludo ya yi nasarar lashewa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Dan takarar jam’iyyar LP a zaben gwamnan Anambra, George Moghalu, ya bayyana dalilin da ya sa ya sha kaye a rumfar zabensa.
A rumfar zaben ta 017, wadda ke da masu kada kuri’a 463, mutane 86 ne kawai suka kada kuri’a a zaben gwamnan na ranar, 8 ga watan Nuwamban 2025.

Source: Twitter
Dr. George Moghalu ya bayyana dalilin faduwarsa ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Sunday Politics' na tashar Channels Tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Moghalu ya fadi a rumfar zabensa
Dan takarar jam’iyyar APGA, Gwamna Chukwuma Soludo, ne ya samu nasara da kuri’u 57 a rumfar zaben, yayin da Moghalu na LP ya samu 22.
A ranar Lahadi, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Chukwuma Soludo na APGA a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 422,664.
Nicholas Ukachukwu na APC ya zo na biyu da kuri’u 99,445, yayin da Paul Chukwuma na YPP ya zo na uku da 37,753.
George Moghalu na LP ya kare a matsayi na hudu da kuri’u 10,576.
Me yasa dan takarar LP ya sha kashi?
Moghalu ya ce dalilin rashin nasararsa shi ne saboda ya ki shiga harkar sayen kuri’u, don kuwa ba shi da kudin da sauran ‘yan takara ke amfani da su wajen jan hankalin masu kada kuri’a.

Kara karanta wannan
Zaben Anambra: Dan takarar jam'iyyar Labour ya barranta da sakamakon zaben gwamna
“Eh, saboda ban iya biyan irin abin da ake biya ba. Ban biya ba, kuma na ki yarda na shiga cikin tsarin. Na ki shiga harkar sayen kuri’a."
“Sun yi amfani da kudi masu yawa wajen sayan kuri’u, me kake tsammanin mutane su yi? Tunda da dama daga cikinsu talakawa ne, sai suka amsa kudin.”
- Dr. George Moghalu
Moghalu ya zargi jam’iyyar APGA mai mulki da shirya yawancin sayen kuri’un da aka gani a zaben.
“Wasu daga cikin jami’an jam’iyyar da aka kama suna sayen kuri’u an gan su suna sanye da tambarin jam’iyyar APGA. Akwai ma kwamishina da aka gani a bidiyo yana sayen kuri’u a mazabata ta."
- Dr. George Moghalu

Source: Twitter
Dan takarar na LP ya kara da cewa zaben gwamnan Anambra bai nuna ainihin zabin jama’a ba, yana mai cewa da zaben ya kasance cikin gaskiya, adalci, kuma babu kudi a ciki, da shi ne zai yi nasara.
Soludo ya yabawa Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan
Zaben Anambra: Dan takarar ADC ya gano lam'a a zabe, ya ce bai gamsu da sakamako ba
Gwamna Soludo ya kwararp yabo ga Shugaba Tinubu ne kan yadda ya tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe a jihar.
Soludo ya kuma bayyana cewa shugaban kasan ya nuna cewa shi cikakken dan dimokuradiyya ne mai bin ta sau da kafa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
