Abdulmumin Kofa Ya Koma APC, Ya Tara Malamai a Kano Sun Yi wa Tinubu Addu'a

Abdulmumin Kofa Ya Koma APC, Ya Tara Malamai a Kano Sun Yi wa Tinubu Addu'a

  • Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya koma jam’iyyar APC bayan korarsa daga NNPP
  • Ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin NNPP da tafiyar Kwankwasiyya don goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Fiye da malamai 2,000 daga yankinsa sun yi addu’o’i na musamman domin nasarar Tinubu da zaman lafiya a Kano da Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC bayan wata biyu da korarsa daga NNPP.

Jibrin Kofa, wanda aka kora daga NNPP bisa zargin yin ayyukan da suka saba wa jam’iyyar, ya tabbatar da dawowarsa APC ne a ranar Litinin yayin wani gagarumin taro a Kano.

Abdulmumin Jbrin Kofa
Abdulmumin Kofa yayin komawa APC a Kano. Hoto: Abdulmumin Jibrin
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan sauya shekar ne a wani sako da Hon. Kofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

'Wane hali muke ciki,' Tsohon hadiminsa ya nemi Tinubu ya yi bayani kan barazanar Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdulmumin Jibrin Kofa ya koma APC

Hon. Kofa ya ce shi da magoya bayansa sun yanke shawarar barin NNPP da tafiyar Kwankwasiyya domin hada kai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen tabbatar da tazarcensa a 2027.

Jibrin ya ce:

“A yau, cikin hadin kai, dubban magoya bayana sun taru a garin Kofa, Bebeji, inda muka yanke shawarar barin NNPP da tafiyar Kwankwasiyya.
"Mun koma jam’iyyar APC, tare da mara wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya don tazarcensa.”

Ya bayyana cewa wannan mataki ya samo asali ne daga tattaunawa da magoya bayansa da kuma fatan ganin ana ci gaba da samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Jibrin ya kara da cewa:

“Na yanke shawarar kawo wannan taron jama’a domin gyara kuskuren da na taba yi a baya na sauya sheka ni kadai. Ban so a ce bana da magoya baya.”

Malamai sun yi wa Tinubu addu'a a Kano

Kara karanta wannan

Rubutu a Facebook ya jefa 'yan Kwankwasiyya 2 a gagarumar matsala a Kano

A yayin taron da aka gudanar a Kofa, fiye da malamai 2,000 daga mazabar Kiru/Bebeji sun gudanar da addu’o’i na musamman domin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Leadership ta rahoto cewa malaman sun yi adduo'i domin neman zaman lafiya da ci gaban Kano da Najeriya baki daya.

Jibrin Kofa, Bola Tinubu
Abdulmumin Kofa a lokacin da ya ziyarci Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Tarihin korar Hon. Kofa daga NNPP

A farkon shekarar nan ne jam’iyyar NNPP ta kori Abdulmumin Jibrin daga cikin mambobinta bisa zargin yin ayyuka da suka saba wa manufar jam’iyyar da kin biyan kudin jam'iyya.

Tun bayan korar, shiru da Jibrin ya yi ya jawo rade-radi a Kano da Abuja cewa yana shirin komawa APC, musamman ganin yadda yake da kusanci da Bola Tinubu.

APC ta ce za ta kwace Kano a 2027

A wani labarin da ya shafi siyasar Kano, mun kawo muku cewa jam'iyyar APC ta sha alwashin kwace jihar daga hannun NNPP a 2027.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas ne ya bayyana haka yayin wani taro a jihar Kano.

Abdullahi Abbas ya yi magana ne yayin da siyasar Kano ke kara daukar zafi musamman kan zaben gwamnan 2027 tsakanin NNPP da 'yan adawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng