Zabubbukan da APC Ta Sha Kashi Tun Bayan Hawan Shugaba Tinubu

Zabubbukan da APC Ta Sha Kashi Tun Bayan Hawan Shugaba Tinubu

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta shiga wasu zabubbuka tun bayan hawan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan mulki a Najeriya.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Wadannan zabubbukan sun hada da na gwamna, 'yan majalisar dokoki na jihohi, 'yan majalisar wakilai da Sanatoci.

Jam'iyyar APC ta yi rashin nasara a wasu zabubbuka
Shugaba Bola Tinubu tare da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @aonanuga1956, @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Legit Hausa ta yi duba kan zabubbukan da APC da 'yan takararta suka sha kashi a mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Tun bayan hawan mulkin Shugaba Tinubu dai mafi yawan zabubbukan da aka gudanar na cike gurbi ne.

APC ta yi rashin nasara a wasu zabubbuka

Zaben gwamnan jihar Anambra ne kadai wanda ba na cike gurbi ba a jerin zabubbukan da aka gudanar a mulkin Mai girma Tinubu.

Duk da cewa APC ta lashe mafi yawa daga cikin zabubbukan, akwai wadanda jam'iyyar da 'yan takararta ba su kai labari ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi magana kan zaben Anambra, ya aika sako ga Gwamna Soludo

Ga jerin zabubbukan da APC ba ta yi nasara ba:

1. Zaben gwamnan Anambra

Jam'iyyar APC ta sha kashi a zaben gwamnan jihar Anambra da aka gudanar a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.

Jaridar The Punch ta ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ayyana Gwamna Chukwuma Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra.

Soludo ya samu jimillar kuri’u 422,664, inda ya doke abokin karawarsa Nicholas Ukachukwu na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 99,445, sai dan jam’iyyar YPP, Paul Chukwuma, wanda ya samu kuri’u 37,753.

2. Zaben mazabar Ibadan ta Arewa a Oyo

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da Folajimi Oyekunle na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Ibadan ta Arewa ta majalisar wakilai.

A cewar sakamakon da INEC ta bayyana, Hon. Oyekunle ya samu kuri’u 18,404, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Hon. Adewale Olatunji (Murphy) na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 8,312, The Nation ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Anambra: Yadda APGA ta samu kuri'u 422664 a kananan hukumomi 21

Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Abiodun Oluwadare daga jami’ar Ibadan, ya bayyana sakamakon a cibiyar tattara sakamako da ke makarantar sakandare ta Ikolaba, Ibadan.

3. Zaben mazabar Bagwai/Shanono a Kano

Jam’iyyar NNPP ta lashe zaben cike gurbi na mazabar Bagwai/Shanono ta majalisar dokokin jihar Kano, cewar rahoton jaridar TheCable.

Jami’in tattara sakamakon zaben na INEC ya bayyana Ali Hassan Kiyawa na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u 16,198.

Ali Hassan Kiyawa ya doke Ahmad Muhammad Kadamu na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 5,347.

An gudanar da zaben cike gurbin ne bayan rasuwar tsohon dan majalisar APC, Halilu Ibrahim Kundila, a watan Afrilun shekarar 2024.

Jam'iyyar APC ta yi rashin nasara a zaben gwamnan Anambra
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda tare da sauran shugabannin jam'iyyar Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

4. Zaben mazabar sanatan Anambra ta Kudu

Chief Emma Nwachukwu na jam’iyyar APGA ya lashe zaben cike gurbi na mazabar sanatan Anambra ta Kudu a jihar Anambra, cewar rahoton jaridar Premium Times.

Sakamakon da hukumar INEC ta sanar, ya nuna cewa Chief Nwachukwu ya samu kuri’u 90,408, inda ya doke babban abokin hamayyarsa Chief Azuka Okwuosa na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 19,812.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Soludo ya lallasa APC, LP, ya ci zabe a dukkan kananan hukumomi 21

An gudanar da zaben cike gurbin ne saboda mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah na jam'iyyar APC, wanda yake wakiltar yankin Anambra ta Kudu a majalisar dattawa.

5. Zaben mazabar Onitsha ta Arewa 1 a Anambra

Ifeoma Azikiwe ta jam’iyyar APGA ta lashe zaben cike gurbi na mazabar Onitsha ta Arewa 1 ta majalisar dokokin jihar Anambra.

Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Ibiam Ikwo-Ekpe n nami’ar fasaha ta tarayya, Owerri, ne ya sanar da sakamakon da yammacin ranar Asabar, 16 ga watan Agustan 2025, jaridar The Cable ta kawo rahoton.

Ifeoma Azikiwe ta samu nasara da kuri’u 7,774, inda ta doke Mrs. Justina Azuka ta jam’iyyar ADC wacce ta samu kuri’u 1,909.

Dan takarar APC, Ezennia Ojekwe, ya samu kuri'u 1,371 yayin da takwaransa na jam'iyyar YPP ya samu kuri'u 655.

Tinubu ya taya Soludo murnar lashe zabe

A wani labarin kuma kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika sakon taya murna ga Gwamna Chukwuma Soludo kan nasarar da ya samu.

Shugaba Tinubu ya taya Gwamna Soludo murna ne kan nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Anambra: An fadi yawan ƙananan hukumomi da Soludo ya lashe, ya nakasa APC

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa nasarar ta tabbatar da cewa tsare-tsaren gwamnatinsa suna haifar da sakamako mai kyau ga al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng