Bayan Shan Kaye a Zaben Anambra, PDP Ta Tsayar da Ɗan Takarar Gwamnan Ekiti
- Dr. Wole Oluyede ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na PDP, wanda zai fafata a zaben gwamnan jihar Ekiti na 2026.
- An rahoto cewa Dr. Wole Oluyede ya samu kuri’u 279, wanda ya ba shi damar doke Funso Ayeni wanda ya samu 239 kuri’u
- PDP ta sha alwashin hambarar da APC a zaɓen 2026, yayi da ta zargin Gwamna Oyebanji da rashin iya shugabanci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti - Wani kwararren likita kuma ɗan siyasa, Dr. Wole Oluyede, ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar gwamnan jihar Ekiti na jam’iyyar PDP.
Dr. Wole Oluyede yanzu ya zama dan takarar PDP a zaben gwamnan Ekiti da hukumar INEC za ta gudanar a ranar 20 ga Yuni, 2026.

Source: Twitter
PDP ta zabi dan takararta na zaben Ekiti

Kara karanta wannan
Zaben Anambra: Dan takarar jam'iyyar Labour ya barranta da sakamakon zaben gwamna
Jaridar Punch ta rahoto cewa Dr. Oluyede ya samu nasara ne a zaɓen fitar da gwanin da PDP ta gudanar daga ranar Asabar zuwa safiyar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa ya samu kuri’u 279, wanda ya ba shi damar doke Funso Ayeni wanda ya samu 239 kuri’u, da kuma Funmilayo Ogun da ta samu kuri'u 17.
Shugaban kwamitin zaɓen fitar da ɗan takarar PDP, Sanata Ibrahim Dankwabo, ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana, yana mai cewa wannan ya nuna cewa PDP jam’iyya ce mai tsari da kwanciyar hankali.
“Mun shaida zaɓe mai gaskiya da lumana wanda ya nuna yadda PDP ke mutunta ƙa’idodi da dimokuraɗiyya. Wannan abin koyi ne ga sauran jam’iyyu,” in ji Sanata Dankwabo.
Ekiti: PDP ta gargadi APC kan zaɓen 2026
Bayan zaɓen, PDP ta bayyana cewa nasarar Oluyede ta zama tamkar sabon babi ga siyasar Ekiti, inda ta yi iƙirarin cewa jam’iyyar ta shirya karɓe mulki daga hannun APC a 2026.
Mai magana da yawun PDP a yankin Kudu maso Yamma, Chief Sanya Atofarati, ya ce zaɓen ya nuna cewa jam’iyyar ta fi APC kwarewa da tsari.

Kara karanta wannan
Zaben Anambra: Dan takarar ADC ya gano lam'a a zabe, ya ce bai gamsu da sakamako ba
“PDP ta sake tabbatar da kanta a matsayin jam’iyyar da ke mutunta tsarin dimokuraɗiyya. Nasarar Dr. Oluyede ta nuna cewa mutanen Ekiti sun gaji da rashin nagartaccen shugabanci da matsalar tsaro da gwamnatin APC ta haifar tun daga 2018,” in ji Atofarati.
Ya kuma ce, nasarar Oluyede ta jefa fargaba a cikin jam’iyyar APC, musamman ganin yadda gwamnatin Oyebanji ke fama da rikice-rikice da rashin daidaito a harkokinta.

Source: Twitter
PDP ta nemi hadin kan 'ya'yanta
A ƙarshe, Atofarati ya yaba wa sauran ‘yan takarar PDP da suka shiga zaben fitar da gwanin bisa natsuwa, haɗin kai da fahimtar da suka nuna bayan zaɓen.
“Wannan nasarar tamu ce gaba daya. Aikin da ke gabanmu ya zarce wannan – dole mu haɗa kai domin mu tabbatar da cewa PDP ta dawo da martabar Ekiti ta hanyar adalci da shugabanci nagari."
- Chief Sanya Atofarati.
PDP ta sha kaye a zaben jihar Anambra
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar PDP, APC, LP, ADC sun sha kaye a zaben gwamnan jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar.
Gwamna Charles Soludo na jam'iyyar APGA ne ya lashe dukkanin kananan hukumomi 21 na Anambra, kamar yadda INEC ta bayyana.
Hukumar INEC ta sanar da cewa APGA ta samu kuri’u 422,664, yayin da APC ta samu 99,445, LP 10,505, sannan PDP ta samu kuri'u 1,401 kacal.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
