Anambra: Bayan Kai Ruwa Rana, INEC Ta Sanar da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna

Anambra: Bayan Kai Ruwa Rana, INEC Ta Sanar da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna

  • A karshe, Hukumar INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Anambra da aka yi a karshen mako
  • INEC ta ayyana cewa jam’iyyar APGA ce ta fi samun kuri'u a zaben gwamnan Anambra da aka gudanar ranar Asabar 8 ga watan Nuwambar 2025
  • Soludo ya samu kuri’u mafi yawa inda ya doke dan takarar APC. Nicholas Ukachukwu da dan YPP, Paul Chukwuma na uku

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra.

Hukumar ta ayyana Gwamna Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Anambra da aka gudanar ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025.

An sanar da sakamakon zaben gwamnan Anambra
Jerin wadanda suka nemi gwamna a zaben Anambra. Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo, Nicholas Ukachukwu.
Source: Twitter

Anambra: Yawan kuri'u da yan takara suka samu

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Anambra: Yadda APGA ta samu kuri'u 422664 a kananan hukumomi 21

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Edoba Omoregie, a cibiyar INEC da ke Awka, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Soludo ya samu jimillar kuri’u 422,664, inda ya doke abokin karawarsa Nicholas Ukachukwu na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 99,445, sai dan jam’iyyar YPP, Paul Chukwuma, wanda ya samu kuri’u 37,753.

A cewar INEC, ‘yan takara 16 ne suka shiga zaben daga jam’iyyu daban-daban, jimillar masu kada kuri’a da aka yi rajista sun kai 2,788,864, yayin da wadanda aka tantance suka kada kuri’a suka kai 598,229.

Hakazalika, jam'iyyar LP ta samu kuri'u 10,505 a zaben yayin da PDP ta samu kuri'u 1,401, mafi kankanta a kuri'un da manyan jam'iyyun adawa a jihar suka samu sai dan takarar ADC ya samu kuri'u 8,317.

Gwamna Soludo ya lashe zaben gwamna a Anambra
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo. Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo.
Source: Facebook

Yawan kuri'u da aka kada a zabe Anambra

An bayyana cewa an kada kuri’u 595,298, daga cikinsu an soke kuri’u 11,244 saboda matsaloli daban-daban a wasu rumfunan zabe a kananan hukumomi hudu.

Farfesa Omoregie ya bayyana cewa an samu wasu wurare da aka soke kuri’u 10,481, amma hakan bai shafi sakamakon gaba ɗaya ba.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Soludo ya lallasa APC, LP, ya ci zabe a dukkan kananan hukumomi 21

Ya kara da cewa:

“Zaben ya kasance cikin lumana kuma bayan kammala kidayar sakamakon, Farfesa Chukwuma Soludo na APGA wanda ya fi kowa samun kuri’u ya lashe zaben.”

Soludo ya samu nasarar lashe duka kananan hukumomi 21 na jihar Anambra, abin da ya tabbatar da galabarsa da babban rinjaye a wannan zabe.

APC, LP da ADC sun sha kaye a Anambra

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Charles Soludo ya doke George Moghalu na LP da John Chuma-Nwosu na ADC a mazabarsu ta Nnewi ta Arewa.

An sanar da cewa Soludo ya samu kuri’u 20,320 yayin da Moghalu ya samu 1,140, shi kuma Chuma-Nwosu ya samu 553.

Nicholas Ukachukwu na jam'iyyar APC mai mulki shi ma ya sha kaye a mazabarsa ta Nnewi ta Kudu inda Soludo ya samu 17,286 kuri’u.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.