Aiki Ya Zo Karshe, INEC Ta Dora Kaso 99% na Sakamakon Zaben Gwamnan Anambra a IReV
- Jami'an wucin gadi da INEC ta dauka domin gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra sun kusa kammala aikin da aka dora masu
- Bincike ya nuna cewa zuwa karfe 9:00 na daren ranar Asabar, INEC ta dora kaso 99.09 na sakamakon zaben gwamnan a shafin IReV
- Wannan dai na zuwa ne bayan manyan yan takaran da suka fafata zaben ciki har da Gwamna Soludo sun koka da sayen kuri'u
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗora sakamakon zaɓen gwamnan jihar Anambra kaso 99.09 a shafinta na yanar gizo watau IReV.
Wannan na zuwa ne bayan kammala kada kuri'a a zaben gwamnan da ya gudana a kananan hukumomi 21 ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025.

Source: Facebook
Binciken da tashar Channels Television ta yi a shafin IReV da misalin ƙarfe 9:12 na daren Asabar ya nuna cewa an riga an ɗora sakamakon zaɓe daga rumfuna 5,668 cikin 5,720 (99.09%).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi zabe cikin lumana a Anambra
Zaɓen wanda aka fara da misalin ƙarfe 8:00 na safe, ya gudana cikin natsuwa da kwanciyar hankali, sai dai rahotanni sun nuna cewa an samu matsalolin sayen ƙuri’u da ƙarancin fitowar masu zaɓe.
Wasu daga cikin ‘yan takara da suka fafata a zaben sun yi zargin cewa abokan adawarsu sun yi amfani da kudi wajen sayen kuri'un jama'a.
Daga cikin wadanda suka yi wannan korafi akwai Gwamna mai ci, Charles Soludo na jam’iyyar APGA, da Nicholas Ukachukwu na APC.
Gwamna Soludo ya zargi yan adawa
Bayan ya kada kuri'arsa, Gwamna Soludo ya ce:
“Labarin da muka ji wanda ke damun mu shi ne cewa wata jam’iyya (ya yi dariya) ta riga ta rubuta sakamakon zaben, ta shirya sauya takarda idan aka zo wurin tattara sakamako.
"Mun ji cewa har sun yi taro da INEC don a hana ɗora sakamakon zaben kai tsaye a shafin IReV domin su samu damar yin magudi.”
Haka kuma, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya bayyana irin wannan damuwa, yana mai cewa an tafka kura-kurai a zaben Anambra.
“Idan kuka sayar da ƙuri’arku, kun sayar da makomarku, makarantu, asibitoci, ayyuka, da makomar ku gaba ɗaya kun hada kun sayar.
"Wannan ne abin da ya fi damuna. A wasu ƙasashe, har ma da na Afirka ta Yamma da na je don sa ido a zaɓe, ban taɓa ganin irin wannan hali ba, dole a dakatar da shi."
- Peter Obi.

Source: Twitter
Wani mai lura da zaɓe daga Situation Room, Dimma Nwobi, ya tabbatar da cewa an samu lamarin sayan ƙuri’u a wasu rumfuna, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Jami'ar INEC da sume a wurin zabe
A dazu, kun ji labarin cewa wata jami’ar INEC ta yanke jiki ta sume a yayin zaben gwamnan Anambra saboda hayaniya da matsalar na’urar BVAS.
An rahoto cewa jami'ar ta sume ne sakamakon hayaniya da cunkoson jama’a a lokacin da take cikin aiki a rumfar zaben da aka tura ta.

Kara karanta wannan
Hukumar INEC ta dora sama da 75% na sakamakon zaben gwamnan Anambra a shafin IReV
Shaidun gani da ido, sun bayyana cewa, an garzaya jami'ar ta INEC mai suna Miss Blessing Egoigwe zaben zuwa asibiti domin kula da lafiyarta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

