Zaben Anambra 2025: Jami'ar INEC Ta Yanke Jiki Ta Suma Ana tsakiyar Kada Kuri'a

Zaben Anambra 2025: Jami'ar INEC Ta Yanke Jiki Ta Suma Ana tsakiyar Kada Kuri'a

  • Wata jami’ar INEC ta yanke jiki ta sume a yayin zaben gwamnan Anambra saboda hayaniya da matsalar na’urar BVAS
  • Dubban masu jefa kuri’a a Enugwu-Ukwu sun kasa kada kuri’unsu saboda BVAS ta gaza tantance katin masu zabe
  • Hukumar INEC dai ta ce ta dora fiye da 95% na sakamakon zaben gwamnan Anambra a shafinta na IReV da ke intanet

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - An samu tashin hankali a rumfar zabe yayin da jami’ar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta yanke jiki ta sume ana tsakiyar zabe.

An rahoto cewa jami'ar ta sume ne sakamakon hayaniya da cunkoson jama’a a lokacin zaben gwamna na Anambra da aka gudanar a ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025.

Jami'ar INEC ta yanke jiki ta suma ana tsakiyar zaben gwamnan jihar Anambra.
Jami'ar INEC ta na tantance mai kada kuri'a a lokacin zaben jihar Ondo. Hoto: @SituationRoomNg
Source: Facebook

Jami'ar zabe ta yanke jiki ta suma a Anambra

Kara karanta wannan

Reshe zai juye da mujiya, Gwamna mai ci ya zargi 'yan adawa da sake kudi a zabe

Rahoton da kamfanin labarai na Najeriya (NAN) ya fitar ya nuna cewa lamarin ya faru ne a rumfar zabe ta 005, Enugwu-Ukwu, a karamar hukumar Njikoka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa an samu cunkoso da hayaniyar jama'a saboda rashin tangardar da aka samu da na’urar BVAS yayin tantance masu kada kuri'a.

An gano cewa jami’ar, Miss Blessing Egoigwe, ta sume ne yayin da jama’a suka fara hayaniya saboda gazawar na’urar BVAS wajen tantance katin masu zabe da kuma yatsun hannunsu.

Shaidun gani da ido, sun bayyana cewa, an garzaya jami'ar zaben zuwa asibiti domin kula da lafiyarta.

Masu zabe da dama sun kasa kada kuri’a

Fiye da masu zabe 470 a yankin Enugwu-Ukwu Community Ward 2 sun kasa kada kuri’unsu saboda tangardar BVAS. Sababbin masu rajista ne suka fi fuskantar matsalar, inda na’urar ta ki tantance bayanansu.

Wata sabuwar mai zabe, Blessing Okoye, mai shekara 18, ta bayyana takaici kan yadda ta rasa damar yin amfani da 'yanci na zabe.

“Na yi farin ciki da zan fara zabe a yau, amma tangardar BVAS ya hana ni. Ina rokon INEC ta inganta tsarin domin mu matasa mu samu damar kada kuri’a,” in ji Okoye.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta dora sama da 75% na sakamakon zaben gwamnan Anambra a shafin IReV

Haka nan wata mai zabe, Ifeoma Iloeze, mai shekara 55, ta koka cewa ta shafe rana tana jiran damar kada kuri’a amma BVAS ta gaza tantance fuskarta har lokaci ya wuce.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta ce ta dora fiye da 95% na sakamakon zaben Anambra a IReV.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Amupitan ya na jawabi a ofishin hukumar da ke Abuja. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

INEC ta dora 95% na sakamakon zabe

Duk da matsalolin da aka samu a wasu rumfunan zabe, INEC ta tabbatar cewa ta dora fiye da 95% na sakamakon zaben gwamnan Anambra a shafinta na IReV.

Rahoton Punch ya nuna cewa daga cikin rumfunan zabe 5,720, an kammala dora sakamakon rumfuna 5,472, wanda ke nuna ingancin amfani da fasahar zamani ta IReV.

INEC ta kuma tabbatar da cewa sakamakon zaben zai kasance amintacce, kuma za a iya duba shi ta kowace hanya, domin tabbatar da gaskiya da sahihancin tsarin zaben jihar.

APGA ta ci zabe a rumfar dan takarar LP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Charles Soludo ya doke dan takarar LP, George Moghalu, a rumfar zabensa da kuri’u 57.

An rahoto cewa Soludo na jam'iyyar APGA ne ya lashe zabe a rumfar zaben ta Uruagu Ward 1, da ke karamar hukumar Nnewi ta Arewa.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: APGA ta lallasa APC, PDP, ta lashe zabe a rumfar dan takarar LP

A hannu daya, jam’iyyar APC ta yi nasara a rumfar da Peter Obi, ya kada kuri’arsa, a kauyen Amatutu, Agulu, karamar hukumar Anaocha.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com