Hukumar INEC Ta Dora Sama da 75% na Sakamakon Zaben Gwamnan Anambra a Shafin IReV
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara tattarawa da kidaya kuri'un da jama'a suka kada a zaben gwamnan jihar Anambra
- Rahotanni sun nuna cewa zuwa Yammacin yau Asabar, jami'an INEC sun dora kaso 75.86 na sakamakon zaben a shafin yanar gizo watau IReV
- Jama'an Anambra sun kada kuri'a a yau Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025 domin zaben wanda zai jagorance su na shekaru hudu masu zuwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra, Nigeria - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC na ci gaba da tattara sakamakon kuri'un da aka kada a zaben gwamnan jihar Anambra.
A yau Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025, hukumar INEC ta gudanar da zaben gwamnan Anambra, duk da dai rahotanni sun nuna mutane ba su fito kada kuri'a yadda ya kamata ba.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta ruwaito cewa tuni INEC ta fara dora sakamakon zaben da jama'a suka yi a shafinta na tattara sakamako watau IReV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
INEC ta dora 75.86% na sakamako a IReV
Binciken da aka yi da yammacin yau Asabar, misalin karfe 5:10 ya nuna cewa INEC ta dora sakamakon kuri'un da aka kada a rumfunan zabe rumfuna 4,339 daga cikin 5,720 da ake da su a Anambra.
Hakan na nufin INEC ta dora kaso 75.86% na sakamakon zaben da ake dab da kammalawa a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan kammala kada kuri’a wacce rahotanni auka nuna ba a wuce sa’o’i hudu ba.
An ruwaito cewa an gudanar da zaben a dukkanin kananan hukumomi 21 na jihar Anambra a ranar Asabar.
'Dan takarar APC ya ci rumfar zabensa
Gwamna Charles Chikwuma Soludo na jam'iyyar APGA na neman wa'adi na biyu yayin da babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar APC, Nicholas Ukachukwu ke kokarin kwace mulki daga hannunsa.
A wasu daga cikin sakamakon da aka bayyana, dan takarar APC ya yi nasara a rumfar zaɓensa da ke kauyen Umudiala , Osumenyi, a karamar hukumar Nnewi ta Kudu, cewar Premium Times.
A rumfar zaɓensa, INEC ta ce Ukachukwu ya samu ƙuri’u 108, yayin da gwamna mai ci kuma ɗan takarar APGA, Charles Soludo, ya samu ƙuri’u huɗu (4) kacal.

Source: Facebook
Soludo ya zargi 'yan adawa da sayen kuri'u
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo da ke neman tazarce ya zargi jam’iyyar adawa da sayen ƙuri’u a zaɓen gwamnan da aka yi ranar Asabar.
Ya bayyana kwarin gwiwa cewa zai lashe zaɓen idan aka bi dokokin zaɓe da ka’idojin INEC, yana mai cewa rahotanni daga wurare daban-daban sun nuna cewa APGA na kan gaba a ƙananan hukumomi 21.
Gwamnan ya ce an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, sai dai wasu matsaloli sun taso a wurare kamar Olumbanasa, inda BVAS ta samu tangarda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

